Yanzun nan: Sarkin Zazzau ya tube rawanin Ciroman Zazzau
- Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya tube rawanin Ciroman Zazzau Alhaji Sai’du Mai Lafiya
- An sauke Ciroman Zazzau daga matsayinsa bayan zarginsa da ake yi da rashin biyayya da girmama masarautar
- Ya kuma kasance makusancin Sarki Nuhu Bamalli
Sarkin masarautar Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya tsige Ciroman Zazzau Alhaji Sai’du Mai Lafiya daga kujerarsa.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Sarkin ya tube rawanin Ciroman Zazzau ne saboda zargin rashin biyayya da girmama masarautar.
KU KARANTA KUMA: Buhari yayi sharhi akan batutuwan da suke hana matarsa bacci
Ciroman Zazzau mai shekaru 84 a duniya ya kasance daga cikin manyan‘Yan Majalisar Sarki kuma Dan uwan Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli ne na kut-da-kut.
A halin da ake ciki, Ciroma ne kusan babba a jerin ’ya’yan sarki da suka fito daga gidan sarautar Mallawa a Masarautar ta Zazzau.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojoji sun kashe sama da mutane 70 da basu jiba basu gani ba, sun rusa asibitoci; Mazauna Benue
A gefe guda, rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Bauchi ta karrama Mai martaba sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Sulaiman Adamu, saboda asassa zaman lafiya tsakanin mutane a masarautarsa da jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi, Sylvester Abiodun Alabi, wanda ya mika lambar yabon ga sarkin a fadarsa, ya bayyana shi a matsayin mutum mai hada kan al'umma wanda ke jagorancin ganin an samu zaman lafiya a Bauchi.
Kwamishinan ya bawa sarkin tabbacin cewa rundunar za ta cigaba da yin ayyukanta na samar da tsaro ga al'umma da kiyayye dukiyoyinsu game da tabbatar da bin doka da oda.
A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar yan sandan kasar Norway, a ranar Juma'a ta ce ta ci Farai minista Erna Solberg tara saboda karya dokar bada tazara na COVID-19.
An ci tarar Solberg ne bayan ta yi taron bikin zagayowar ranar haihuwarta da iyalanta suka hallarta kamar yadda reuters ta ruwaito.
An ci ta tarar Norwegian crowns 20,000 ($2,352) a cewar shugaban yan sanda, Ole Saeverud kamar yadda ya fada yayin taron manema labarai.
Asali: Legit.ng