Gwamnati Ta Na Hango N12bn Daga Sabon Harajin Motar da Tinubu Ya Kirkiro
- Gwamnatin tarayya ta kawo tsarin biyan kudi duk shekara a matsayin shaidar mallakar abin hawa
- Daga wannan N1000 da za a rika karba, ana tunanin Naira biliyan 12 zai iya shiga asusun gwamnati
- Bincike ya nuna motocin da ake da su a Najeriya sun zarce miliyan 11 tun shekaru biyar da suka wuce
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Gwamnatin tarayya ta na sa ran samun kusan Naira biliyan 12 a shekara daga kudin shaidar POC da za ta rika karba daga hannun mutane.
An fito da harajin shaidar abin hawa watau POC da mutane za su rika biya a Najeriya, Punch ta ce hakan zai kawowa gwamnati biliyoyin kudin shiga.
A tsakiyar shekarar 2018, hukumar NBS mai tattara alkaluma a kasar nan ta yi hasashen cewa akwai motoci fiye da miliyan 11.76 a Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bincike ya nuna a kowace shekara, ana shigo da motoci kusan 400, 000 a Najeriya. Abin da hakan yake nufi shi ne motoci sun karu sosai zuwa yanzu.
An shiga da motoci 306, 000
Motoci 192,287 aka shigo da su ta tashoshin kasar nan daga Junairu zuwa Oktoban 2021, a daidai wannan lokacin an shigo da motoci 114,159 a 2022.
Idan yanzu akwai motoci kusan miliyan 12.1 a tituna, kuma aka yi sa’a mafi yawancin masu amfani da su, su ka biya haraji, za a samu kudin shiga.
Sannan za a karbi wadannan kudi a hannun masu babura zuwa keke napep. Rahotanni sun fito a kan yadda gwamnati za ta mori wannan tsari.
Naira biliyan 12 a shekara
Lissafin da aka yi ya nuna gwamnatin tarayya za ta tashi da kimanin Naira biliyan 12 a shekara. Hakan zai taimaka yayin da gwamnati ke kukan rashin kudi.
Gwamnatin jihar Legas za ta fara karbar wannan sabon haraji na POC mai nuna shaidar mallaka, sai dai har zuwa yanzu sauran jihohi ba su ce komai ba.
Abin da Legit.ng Hausa ba ta da masaniya a kai shi ne yadda za ayi rabon harajin da aka tattara.
Jama'a sun koka da tsarin
A makon da ya gabata ne rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta wajabtawa masu abubuwan hawa biyan haraji domin su mallaki shaidar POC a Najeriya.
Masu tirela, tifa, gingimari, karamar mota, keke napep, babur sai sun biya N1000. Jama’a sun yi tir da tsarin, sun an tatse talaka babu gaira-babu dalili.
Asali: Legit.ng