Ka Zo Ka Kula Da Danka”: Matashiya Fashe Da Kuka Bayan Tsohon Saurayinta Ya Rabu Da Ita Da Ciki

Ka Zo Ka Kula Da Danka”: Matashiya Fashe Da Kuka Bayan Tsohon Saurayinta Ya Rabu Da Ita Da Ciki

  • Wata yar Najeriya da ke dauke da juna biyu ta garzaya soshiyal midiya domin rokon tsohon saurayinta da ya rabu da ita
  • Yayin da take bayyana cewa ba wai nema take yi ya dawo cikin rayuwarta ba, ta ce kawai rokonsa take yi ya zo ya kula da dansa
  • Ta koka kan yadda take cikin mawuyacin hali saboda ita ke daukar dawainiyar cikinta ita kadai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiya yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya bayan da tsohon saurayinta ya dankara mata ciki.

A wani bidiyo mai tsuma zuciya da ta wallafa a TikTok, matashiyar ta roki tsohon saurayinta da ya dauki nauyin dan da take shirin haifa masa.

Matashiya na kuka
Ka Zo Ka Kula Da Danka”: Matashiya Fashe Da Kuka Bayan Tsohon Saurayinta Ya Rabu Da Ita Da Ciki Hoto: @dabbieofficial2
Asali: TikTok

Ta fayyace cewa ba wai tana so ya dawo rayuwarta bane illa kawai tana so ya dauki dawainiyar dan ne kawai.

Kara karanta wannan

“Uwar Miji Ta Ce Ba Zan Taba Haihuwa Ba”: Yar Najeriya Ta Samu Cikin Yan 3, Ta Nuna Wa Duniya

A cewarta, tana cikin kunar rai kuma iyayenta sun bukaci da bar masu gidansu bayan sun gano cewa tana dauke da juna biyu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta cika da mamakin dalilin da yasa tsohon saurayin nata ke gasa mata aya a hannu sannan ta tunatar da shi cewa dan nasa ne.

"Dan Allah na rokeka...Ka zo ka kula da danka....Babu yadda za a yi na samar da dan nan ni kadai...Ba wai ina rokonka ka dawo rayuwata bane kawai abun da nake so shine ka dauki dawainiyar danka shikenan...Na rigada na fuskanci radadi ba kadan ba...Me yasa kake kara jefani cikin wahala...??? #dabbieofficial2 wannan dan naka ne fa... don Allah," ta rubuta.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

maryshieh1 ta ce:

"Ya ke kyakkyawa kada ki roke shi kada ki yi nima na fuskanci haka lokacin da na fi bukatarsa amma kin san wa ya cece ni, Allah ya cece ni."

Kara karanta wannan

"Bayan Wuya": Matashiya Wacce Ke Yawon Talla Ta Koma Turai, Ta Fara Aiki a Matsayin Malamar Asibiti

Abagrant ta ce:

"Yar'uwa, kada ki damu komai zai wuce, ki roki Allah, irin haka na faruwa da ni amma na yi imani da Allah."

Ola mummy ta ce:

"Ba kya bukatar yin kuka a soshiyal midiya wasu mutane basu da imani ki kasance da karfin gwiwa sannan ki tashi tsaye Allah zai kawo maki mataimaki."

Jarumar fim ta saki zafafan hotunanta da mijinta a Saudiyya

A wani labarin kuma, shahararriyar jarumar fina-finan kudu, Mercy Aigbe ta tashi kan masoya da mabiya shafinta na soshiyal midiya inda ta saki zafafan hotunanta da mijinta.

Mercy da angonta dai suna cikin jerin musulman duniya da suka sauke farali a aikin hajjin bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel