Sabon Tsarin CBN Zai Jawo Danyen Tashin Farashin Fetur, Lita Zai Iya Haura N580

Sabon Tsarin CBN Zai Jawo Danyen Tashin Farashin Fetur, Lita Zai Iya Haura N580

  • An fara ganin tasirin karya darajar Naira da barin farashin Dalar Amurka a hannun ‘yan kasuwa
  • Muddin kudin kasashen waje su ka yi tsada, ya zama dole fetur ya tashi domin shigo da shi ake yi
  • Ba da dadewa ba farashin gidajen mai zai rika canzawa idan kudin sari daga tashohi ya lula sama

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Alamu na nuna cewa farashin man fetur zai iya tashi a Najeriya a lokacin da mutane ba su gama farfadowa daga radadin cire tallafi ba.

A makon nan Vanguard ta kawo labari cewa canjin da aka samu na farashin kudin kasar waje zai yi sanadiyyar da litan fetur zai kara tsada sosai.

‘Yan kasuwa sun ce karyewar Naira na da tasiri a kasuwancinsu, farashin da su ke sayen man fetur zai karu, hakan zai canza farashi a gidajen mai.

Kara karanta wannan

AEDC: Kamfani Ya Sanar da Sabon Farashi da Lokacin Ƙara Kuɗin Lantarki a Garuruwa 4

fetur
Man fetur a mota Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

An tsaida farashin kowane lita a kusan N540 ne a lokacin da aka yi lissafin Dalar Amurka a tsohon farashi, kafin bankin CBN ya canza tsari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan kida ya canza, rawa za ta canza

Bincike ya nunawa jaridar cewa mafi yawan masu sarin mai sun canza farashin litarsu zuwa tsakanin N492 da 495 daga N488 da aka saba.

Idan aka leka gidajen mai a Legas, farashi ya fara tashi ya na komawa kimanin N515, a wajen garin kuwa akwai inda ake saida lita fiye da N650.

Manyan dillalai sun ce tun da aka koma saida Dala a kan N770, ya zama dole farashin gidajen mai ya canza, lita za ta kai akalla N550.

Za a fara shigo da fetur

Rahoton ya ce ‘yan kasuwan da aka ba lasisi sun fita sayo man fetur yanzu a ketare.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake Bisa Kuskure, Sun Sace Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

Saboda ganin sun samu riba, kamfanonin su na hada-kai da bankuna domin samun kudin kasashen waje da ake amfani da su wajen ciniki a ketare.

Wasu shugabannin kamfanonin mai da aka yi hira da su, sun shaida cewa za a dauki akalla daga yanzu zuwa Yuli kafin man su ya shigo Najeriya.

Ganin yadda farashi yake canzawa a kasuwa, shugaban DAPPMAN, Olufemi Adewole ya ce ba a tilasta masu saida mai a wani kayadajjen farashi ba.

Motoci za su kara tsada ko kuwa?

Ana haka ne Punch ta ce karyewar Nairan zai jawo motoci su kara tsada a Najeriya domin kudin shigo da su daga ketare zai karu da kimanin 40%.

Hakan ya na zuwa ne bayan an ji labari watakila daga yanzu motoci za su rika barkowa Najeriya daga kasashen waje kamar yadda aka saba a da.

Hana shigo da motoci ta kasa ya jawo hukumar Kwastam ta ga kudin shiga da ake samu ya ja baya. Haka zalika tsarin bai yi wa 'yan kasuwa dadi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng