Duniya Ba Yarda: Jami’an ’Yan Sanda Sun Kama Mai Gadi da Ya Hada Baki Aka Fasa Gidan Da Yake Aiki A Lagos

Duniya Ba Yarda: Jami’an ’Yan Sanda Sun Kama Mai Gadi da Ya Hada Baki Aka Fasa Gidan Da Yake Aiki A Lagos

  • Rundunar 'yan sandan jihar Lagos, ta kama wani mai gadi da ake zargin ya hada baki da wani matashi don yin fashi a gidan da ya ke aiki
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da kama matashi mai suna Tony da ake zargi da fasa gida da kuma yin sata
  • Ana zargin matasan ne da hada baki da kuma fashi da makami bayan sun fasa gidan da Pius ke aikin gadi da ke unguwar Parkview a Ikoyi

Jihar Lagos - Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta kama wani mai gadi da ake zargin an hada baki da shi don gudanar da fashi da makami a unguwar.

Wanda ake zargin mai suna Pius yana gadi a wani gida a unguwar Parkview da ke Ikoyi cikin jihar Lagos.

Kara karanta wannan

Rusau: Abba Kabir Ya Ce Ba Za Su Yi Asara Ba, Zai Yi Amfani Da Burbushin Rushe-rushen Don Gyara Ganuwoyin Kano

'Yan sanda sun kama mai gadi bayan hada baki da yin fashi a Lagos
Wadanda Ake Zargin, Pius Da Tony. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Ana zargin Pius da hada baki da wani mai suna Tony da fasa gidan da yake aiki a cikin unguwar tare da yin sata, Daily Trust ta tattaro.

Hundeyin ya ce an kama mai gadin bayan 'yan sanda sun yi bincike

Kakakin rundunar 'yan sandar jihar, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da hakan inda ya ce Tony shi ne wanda ya fasa gidan tare da satar kayayyaki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ake zargin Pius ta kulla dukkan makarkashiyar da har Tony ya je ya aikata wannan laifi da ake tuhumarsu akai.

Hundeyin ya ce ofishin 'yan sandan yanki na Ikoyi sun samu rahoton faruwar lamarin a ranar Juma'a 16 ga watan Yuni da misalin karfe 1:00 na dare.

Ya kara da cewa, an hada jami'an 'yan sanda cikin gaggawa zuwa wurin da fashin ke faruwa a unguwar Parkview tare da yi wa yankin kawanya.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbe Wani Da Ya Yi Niyyar Tserewa Daga Komarsu, Matashin Ya Tsira Da Raunuka A Kaduna

Ya bayyana yadda aka kama 'yan fashin a jihar Lagos

A cewarsa:

"Bayan bincike mai zurfi, an kama wani daga cikinsu mai suna Tony tare da kayan da ya sata.
"Cikin abubawan da aka samu daga gare shi akwai wayoyin kamfanin Samsung da agogon hannu guda biyar da na'urar daukar hoto da kayan ado a cikin babbar jaka.
"Binciken ya sake ganowa tare da kama wani mai suna Pius wanda ya kasance mai gadi ne a gidan wanda aka yiwa satar."

Hajji: Dubban Maniyyata Sun 'Makale' A Filin Jiragen Sama Da Ke Jihar Legas

A wani labarin, maniyyata da dama sun makale a filin jiragen saman Murtala Mohammed da ke Legas.

Maniyyatan an gano su a kwance a cikin masallaci sun koka kan yadda aka barsu ba tare da jigilar su ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan samun matsalar, an dauki hayar kamfanin Arik Air don jigilarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel