“Mai Laifi Ke Tsoro Na”: Faifan Bidiyon Hirar Bawa Ya Yadu Kafin Tinubu Ya Dakatar Da Shi Daga Shugaban EFCC

“Mai Laifi Ke Tsoro Na”: Faifan Bidiyon Hirar Bawa Ya Yadu Kafin Tinubu Ya Dakatar Da Shi Daga Shugaban EFCC

  • Dakataccen shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci, EFCC, Abdulrasheed Bawa ya ce bai kamata mutane suna tsoron amsa gayyatar EFCC ba
  • Bawa ya ce idan har mutum na tsoron amsa gayyatar hukumar to watakila yana da wasu abubuwa ne da ba zai iya bayyanawa ba
  • Bawa ya yi wannan hirar ne da wani dan jarida, Chude Jideonwo makwanni kadan kafin Sugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi

FCT, Abuja - Dakataccen shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya ce masu laifi ne kadai suke tsoron gayyatar hukumar.

Bawa ya bayyana haka ne yayin hira da dan jarida, Chude Jideonwo da aka wallafa a ranar Litinin 19 ga watan Yuni.

Bawa ya ce masu laifi ne kadai ke tsoron gayyatar hukumar EFCC
Dakataccen Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa. Hoto: EFCC.
Asali: Facebook

Ya ce bai kamata mutum ya ji tsoronsa ko hukumar ba lokacin da aka gayyace shi domin bayani akan wani abu.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An yi ram da wasu mazauna Qatar, rikakkun 'yan safarar kwaya a wata jiha

Bawa ya ce bai kamata wani ya ji tsoron amsa gayyatar EFCC ba

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Aikin mu kawai muke yi, bai kamata wani ya ji tsoro ba, ya zo kawai ba tare da wata fargaba ba, muna karkashin ikon hukuma ne.
"Kawai tambayoyi ne akan wadansu abubuwa da suka faru, meye na tsoro? A wurina ina ga mai laifi ne zai ji tsoron zuwa."

Bawa ya yi wannan hirar ne makwanni kadan kafin Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi a ranar Laraba 14 ga watan Yuni.

Da yake wallafa faifan bidiyon a kafar Twitter, Chude ya rubuta cewa:

"Makwanni kadan da suka wuce, Abdulrasheed Bawa ya bani damar shiga cikin hedkwatar hukumar EFCC wanda ban taba samu ba a Abuja.
"Ta tabbata ita ce hirarsa ta karshe kafin a dakatar da shi a makon da ta gabata."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shin EFCC Ta Ayyana Neman Matawalle Ruwa A Jallo? Gaskiya Ta Fito

Faifan bidiyon ya yadu a kafar sada zumunta

Ku kalli faifan bidiyon a kasa inda Bawa ya ke cewa kada kuji tsoron gayyatar EFCC.

Bawa ya ce ba zai iya cutar da ko kuda ba, amma mutane suna tsoronshi.

Abubuwa 2 Da Ake Tunanin Sune Dalilin Da Suka Sa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Bawa

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya dakatar da shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa daga mukaminsa.

Bawa mai shekaru 43, ya kasance kan karagar mulkin hukumar tun shekarar 2021 lokacin da tsohon shugaban kasa Buhari ya nada shi.

Akwai wasu dalilai guda biyu da ake tunanin su ne musabbabin saka Bola Tinubu dakatar da Bawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel