Bayan Cire Tallafin Fetur, Farashin Lantarki Zai Lula Da Kashi 25 Zuwa 40 Nan Da 'Yan Kwanaki

Bayan Cire Tallafin Fetur, Farashin Lantarki Zai Lula Da Kashi 25 Zuwa 40 Nan Da 'Yan Kwanaki

  • Kudin da ake sayen wutar lantarki zai iya tashi saboda daidaita farashin kudin kasashen ketare
  • Babban bankin CBN ya cire sabani a kasuwar canji, hakan zai jawo canji a bangaren lantarki
  • Mutane za su kara kashe kudi a kan abin da su ka saba kashewa daga farko watan Yuli mai zuwa

Abuja - Akwai yiwuwar farashin shan wutar lantarki ya karu da fiye da 40% nan da wata mai zuwa. Hakan ya na nufin an soke duk wani tallafin shan wuta.

The Guardian ta fitar da rahoto da safiyar Litinin cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta kawo karshen N50bn da ake kashewa a kowane wata a tallafin lantarki.

An yi lissafin Dalar Amurka da kamfanoni a kan N441/$1 ne, sai kuma yanzu bankin CBN ya daidaita kasuwar canji, farashin ya zama iri guda a duk Najeriya.

Kara karanta wannan

IMF Tayi Alkawarin Taimakon Najeriya Ganin Gyare-Gyaren da Bola Tinubu Ya Kinkimo

Lantarki
Na'urorin wutar lantarki Hoto: AFP / FLORIAN PLAUCHEUR
Asali: AFP

Da kudin kasar waje ake amfani wajen tsaida farashin lantarki. Legit.ng Hausa ta fahimci tsarin da aka kawo ya jawo bambancin fiye da N20 a kowace $1.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar ta ce a 2015 an yi lissafi ne a kan N198.97/$, sai aka yi amfani da N383.80/$ a 2020.

Hauhawar farashi da canjin Dala

Yanzu farashin kaya sun tashi da 22.41%, sannan gwamnatin tarayya ta janye tallafin fetur. Masana su na ganin tsadar wuta za ta iya karuwa da 40%.

Dama can hukumar NERC ta yi niyyar cire tallafin shan wutar lantarki daga Yulin 2023, sannan kuma a kara farashin sayen wutan ga rukunin D da E.

A rahoton Nairametrics, masana sun ce tashin farashin da za a samu zai zama tsakanin 25% da 30% idan aka yi la’akari da yadda kasuwa ke tafiya.

Kara karanta wannan

Jerin Jihohin Najeriya 10 Da Suka Fi Fuskantar Hauhawan Farashin Kaya a 2023

Masana irinsu Shugaban kamfanin New Hampshire Capital, Odion Omonfoman su na ganin hauhawar farashin kaya da tashin Dala za su yi tasiri sosai.

Wasu kuma su na da ra'ayin sabuwar dokar wutar lantarki ta 2023 ta kasa ce za ta jawo tashin farashin, hakan bai shafi fadar shugaban Najeriya ba.

A duk yadda abubuwa su ka kasance, mafi yawan ‘yan Najeriya za su sha wahala musamman ganin farashin man fetur ya karu daga watan Mayu.

Barazanar 'yan kwadago

Rahoto ya fito cewa Ƙungiyar ƙwadago ta yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnatin ta yi wasa da buƙatun da ta gabatar mata a baya.

Hakan na zuwa ne yayin da ɓangarorin biyu za su sake zama a ranar Litinin. Shugaba Bola Tinubu ya fito da wasu tsare-tsare bayan shiga ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng