Abokin Cin Mushe Ne: Minista Sirika Ya Tona Asirin Dan Majalisar da Ya Fara Kushe Batun Jirgin Nigeria Air

Abokin Cin Mushe Ne: Minista Sirika Ya Tona Asirin Dan Majalisar da Ya Fara Kushe Batun Jirgin Nigeria Air

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama ya bayyana yadda dan majalisa ya nemi cin hanci daga hannunsa game da jirgin Nigeria Air
  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa kan yadda aka kaddamar da jirgin saman kasar, amma daga baya aka neme shi aka rasa
  • Shugaba Buhari ya sauka daga mulki, abubuwa da yawa na ci gaba da fitowa game da mulkinsa, daga ciki har da lamarin gwamnan CBN

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, ya zargi dan majalisar da ya bayyana batun jirgin kasa na Nigeria Air a matsayin yaudara da neman 5% na kaso biyar na Kamfanin Jirgin Saman Najeriya.

A wani zaman da majalisar wakilai ta yi, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin sufurin jiragen sama, Nnolim Nnaji, ya bayyana batun jirgin saman Najeriya da gwamnatin Buhari ta yi a matsayin yaudara.

Kara karanta wannan

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Dakataccen Gwamnan CBN a Filin Jirgin Sama

Dan majalisar ya caccaki aikin, inda ya soki Gwamnatin Tarayya kan abin da ya bayyana da rashin kwarewa da bani na iya, Punch ta ruwaito.

Batun jirgin Najeriya ya karo tabo liki daga Sirika
Jirgin Nigeria Air da ake ta cece-kuce a kansa | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Yadda ta kaya tsakanin ministan Buhari da dan majalisa

Amma da yake magana a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Arise a ranar Lahadi, Sirika ya ce dan majalisar da ke sukar ya taba tuntubarsa, kana ya nemi a ba shi kashi 5% na kamfanin jirgin saman ga "shi da jama'arsa".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da Reuben Abati, mai gabatar da shirin ya nemi tsohon Ministan ya fayyace ko da gaske dan majalisar ya nemi cin hancin ga kansa ne da sauran ‘yan majalisar, Sirika ya ce:

“A yi adalci, Hon Nnaji bai ce sauran mambobi ba. Ya ce yana so ne wa kansa da jama'arsa. Mutanensa na iya zama danginsa, suna iya zama membobi kuma suna iya zama jagorori.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi 'Yan Takarar da Sanatoci da 'Yan Majalisar Wakilan Jiharsa Zasu Zaɓa a Majalisa Ta 10

"Ban sani ba, amma ya dage a ba shi kashi 5% na ce ya kwantar da hankali ya tunkari masu abin. Abin da na gaya masa ke nan."

Tsohon Ministan ya kuma soki Nnaji da kwamitin kula da zirga-zirgar jiragen sama bisa jawo cece-kuce kan lamarin, Daily Trust ta ruwaito.

Rashin gaskiya ya sa Tinubu ya sallammi gwmanan CBN

A wani labarin, shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana dakatar da gwamnan CBN, Godwin Emefiele bisa wasu dalilai.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnati na kan bincike ne kan halin da ake ciki a babban bankin da kuma tattalin arziki.

Daraja da tattalin arzikin Najeriya ya sauka sosai a tsawon shekaru kusan tara da Emefiele ya yi a gwamnan CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel