Tallafin Mai: Kamfanin Najeriya, Innoson Ya Kero Motoci Masu Hasken Rana Da Iskar Gas

Tallafin Mai: Kamfanin Najeriya, Innoson Ya Kero Motoci Masu Hasken Rana Da Iskar Gas

  • Kamfanin Innoson Motors ya ƙero motoci masu amfani da iskar gas yayin da ‘yan Najeriya ke kokawa kan matsalar cire tallafin man fetur
  • Kamfanin ya ce ya ƙera dogayen bas, kananan bas, motocin hawa, da manyan motoci da za su riƙa amfani da iskar gas
  • Ya bayyana cewa motocin nasa sun fi na man fetur inganci, sannan za su taimaka wajen kare muhalli

Anambra - Kamfanin ƙera motoci na ɗan Najeriya, Innoson Motors, ya fitar da sabbin motocin bas masu amfani amfani iskar gas da kamfanin ya samar.

Kamfanin ya bayyana a shafinsa na Fesbuk cewa motocin da ya ƙero sun haɗa da manyan motoci, ƙananan bas, motocin daukar marasa lafiya, da kuma dogayen bas.

An fara kera motoci marasa amfani da fetur a najeriya
An fara kera motoci masu amfani da iskar gas a Najeriya. Hoto: Innoson Vehicles
Asali: Facebook

Innocent Chukwuma ya yi bayani kan motocin masu amfani da iskar gas

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Kungiyar ASUU Ta Bayyana Matsaya 1 Tilo Kan Tallafin Man Fetur a Najeriya

Innocent Chukwuma, wanda shi ne mai kamfanin, kuma babban jami'i a ciki, ya ce motocin suna da inganci sosai, kuma an yo su ne daidai da amfani a kan hanyoyin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Muna ƙera su ne bisa ga yadda ake buƙatarsu, mun ƙera waɗannan bas ɗin ne saboda akwai bukatarsu a yanzu. A lokacin annobar COVID-19, mun samar da motocin ɗaukar marasa lafiya da dama, don haka muna nan koda yaushe, a shirye muke mu ƙera."
"Motoci masu amfani da iskar gas (CNG) suna magance matsalar dogaro da nau'in mota kala ɗaya ko biyu ma."

Ya ƙara da cewa sun kuma ƙera motocin ne ta yanda zaka iya sanya musu iskar gas, man dizel, da kuma fetur, ya danganta ga wanda ka samu a inda kake.

Sannan ya kuma ce, kamfanin nasu na ƙera ƙarin motoci kala daban-daban da suka haɗa da masu amfani da wutar lantarki, gas, da ma masu amfani da hasken rana.

Kara karanta wannan

NCC Ta Ba MTN, Airtel, Glo, 9mobile Wa'adin Daina Amfani Da Tsofaffin Lambobin Sa Kati, Data Da Sauransu

Gwamna Soludo ya yaba wa Innoson

Chukwuma Soludo, gwamnan jihar Anambra, ya ce jihar na shirye-shiryen samar da hanyoyin magance ƙalubalen da ake fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur.

Guardian ta yi rahoto cewa Soludo ya samu wakilcin kwamishinan masana’antu na jihar, Christian Udechukwu a wajen ƙaddamar da motocin.

Gwamnan ya ce akwai buƙatar 'yan ƙasa su dage da bunƙasa masana'antu na cikin gida domin taimakawa gwamnati wajen samun kuɗaɗen shiga, kamar yadda Innoson ya ke yi.

Ya ƙara da cewa Innoson yana da fasahohin sosai na samar da nau'o'in motocin da za su yi matuƙar taimakawa harkar sufuri a Najeriya.

Gwamnan ya kuma ce masana'antu na cikin gida irin waɗannan za su taimakawa Najeriya wajen rage yawan basussukan da ake bin ta.

Gwamnonin Najeriya sun bayyana matsayarsu kan batun cire tallafin man fetur

A wani labarin na daban da Legit.ng ta wallafa, ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta ziyarci shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, inda suka bayyana goyon bayansu dangane da tallafin man fetur da ya cire.

Kara karanta wannan

NNPC Ya Yi Fashin Baki Kan Dalilan Cire Tallafi Da Kuma Karin Farashin Man Fetur

Gwamnonin sun kuma yabawa Tinubu kan tsare-tsaren da gwamnatinsa ke shirin zuwa da su na ci gaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel