NNPC Ya Yi Fashin Baki Kan Dalilan Cire Tallafi Da Kuma Karin Farashin Man Fetur

NNPC Ya Yi Fashin Baki Kan Dalilan Cire Tallafi Da Kuma Karin Farashin Man Fetur

  • Kamfanin NNPC na ƙasa ya bayar da takaitattun bayanai kan dalilin cire tallafin man fetur da FG ta yi da kuma ƙarin farashin man da ya biyo baya
  • Kamfanin ya ce tun a watan Maris ɗin 2023, ake bin Gwamnatin Tarayya bashin N2.8tr
  • Ya kuma ƙara da cewa ba zai daidaita farashin man ba, saboda kasuwa za ta gyara farashin da kanta a kowane lokaci

Cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi bai yi wa 'yan Najeriya da dama daɗi ba, musamman ma yadda hakan ya jaza hauhawar farashin man.

Duk da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ci gaba da jaddada buƙatar cire tallafin, ta kasa magance matsalar tattalin arziƙin da ke addabar ‘yan Najeriya da ‘yan kasuwa.

A ƙoƙarin wayar da kan ‘yan Najeriya kan dalilin cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi da kuma ƙarin farashin man da aka samu, kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), ya yi ƙoƙarin amsa tambayoyin da ake yawan yi dangane da batun wanda ake yawan tafka muhawara a kai.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ma'aikatan Shari'a Na Kasa Sun Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur

NNPC ya yi bayani kan cire tallafin man fetur
NNPC ya yi talkaitaccen bayani kan cire tallafi da hauhawar farashin man fetur. Hoto: NNPC LTD
Asali: UGC

Me yasa farashin man fetur ya ƙaru kafin watan Yuni?

Da yake amsa tambayoyi dangane da dalilin da ya sa aka ƙara farashin man fetur kafin watan Yuni da ya kamata tallafin man fetur ɗin ya ƙare, NNPC ya ce ana bin Gwamnatin Tarayya bashin N2.8tr a watan Maris din 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewa jinkirin kawar da tallafin man fetur har zuwa ƙarshen watan Yunin 2023, na iya haifar da karancin man fetur da kuma jefa mutane cikin wahala, saboda 'yan kasuwa za su iya gaza samar da wadataccen man fetur a lokacin.

Me yasa ake sayar da tsohon man fetur akan sabon farashi?

Da yake magana kan dalilin da ya sa kamfanin na NNPC ke sayar da tsohon man fetur a kan sabon farashi, ya bayyana cewa idan gidajen mai suka ci gaba da sayar da shi a kan tsohon farashin, ba za su iya sawo man a gaba ba, wanda a ƙarshe hakan zai haifar da ƙarancin man fetur a faɗin kasar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Labule Da Kungiyar Ma'aikata Ta Kasa Kan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito

Shin farashin man fetur zai ci gaba da hauhawa ne?

Dangane da tambayar, idan farashin man fetur zai ci gaba da hauhawa kamar yadda muka gani a cikin ‘yan kwanakin da aka cire tallafin, kamfanin NNPC ya amsa da cewa, kasuwa ce za ta daidaita farashin a kowane lokaci.

Ya ce tunda an samu ƙaruwar sabbin masu kasuwancin man, to dole kasuwar za ta daidaita.

Don haka, farashin da yake a yanzu na ɗan lokaci ne kawai, cikin mako ɗaya zuwa biyu, za'a iya samu sauyin farashi, tunda manyan 'yan kasuwa sun shigo cikin harkar.

Me ya sa NNPC ya bayyana sabon farashi?

Da yake magana kan dalilin da ya sa NNPC ya bayyana sabon farashin man fetur a fadin Najeriya, kamfanin ya ce ba ya da alhakin tsaida farashin man fetur a cikin masana'antar. Hakazalika ma ga sauran kamfanoni, NNPC na bayyana farashin man fetur ne daidai da yanayin kasuwa.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Man Fetur: Babban Basarake Ya Ba Shugaba Tinubu Wata Muhimmiyar Shawara

Shin NNPC ne kaɗai zai ci gaba da samar da man fetur?

Wata tambayar da aka gabatar ita ce ko NNPC zai ci gaba da zama kamfani ɗaya tilo da zai riƙa samar da man fetur, inda kamfanin ya amsa da cewa a'a, sannan ya ƙara da cewa bisa doka, babu wani kamfani da ke da damar sarrafa sama da kashi 30 cikin 100 na kasuwar.

Ta ya ya za a kare masu amfani da man fetur ɗin?

Tunda kamfanin NNPC Ltd yanzu yana aiki a matsayin kamfani mai zaman kansa kuma mai taka rawa a harkar mai da iskar gas, ta yaya za a kare masu amfani da mai?

Kamfanin ya bayyana cewa akwai hukumomin da ke kula da masana'antu, waɗanda za su riƙa kula da kare masu amfani da man, kamar hukumar kula da man fetur ta Najeriya (NMDPRA) da kuma hukumar kare masu amfani ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Kamar Najeriya, Wata Kasar Afrika Ta Sanar Da Rage Tallafin Man Fetur, Ta Bayar Da Dalilanta

Makomar samar da mai ga kasuwannin cikin gida

Daga ƙarshe, kamfanin ya yi ƙarin haske kan makomar samar da man fetur a kasuwannin cikin gida, inda ya ce kamfanin mai na NNPC, matatar man Dangote, da sauran matatun mai na cikin gida za su tabbatar da cewa an samu wadataccen man fetur da kuma samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya.

Bugu da ƙari, za su kawowa Najeriya ƙarin shigowar kuɗaɗen ƙasar waje da ta ke samu, da kuma kara haɓaka arzikin cikin gida (GDP).

Atiku ya soki Tinubu kan yadda ya cire tallafin man fetur

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya soki tsarin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bi na cire tallafin man fetur da ya yi bayan rantsar da shi.

Atiku ya bayyana cewa dole ne sai gwamnati ta ɗauki wasu muhimman matakai gabanin ya sanar da cire tallafin man fetur ɗin.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC Kyari, Ya Bayyana Babban Dalilin Da Ya Sa Dole a Cire Tallafin Man Fetur

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng