Kungiyoyi Sun Nemi Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa Ya Sauka Domin Yin Bincike a Kansa

Kungiyoyi Sun Nemi Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa Ya Sauka Domin Yin Bincike a Kansa

  • Gamayyar ƙungiyoyi masu fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa sun nemi shuganaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ya sauka daga muƙaminsa
  • Ƙungiyoyin da suka haɗa da ta matasan Arewa, matasan Neja-Delta sun zargi shugaban na EFCC da nuna wariya da bita da ƙulli wajen binciken masu laifuka
  • Sun kuma yi kira ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ba da muhimmanci sosai wajen yaƙi da cin hanci da rashawa

Gamayyar ƙungiyoyi da suka haɗa da ƙungiyar matasan Neja-Delta (NDYC), ƙungiyar matasan arewa (NYF), ƙungiyar juyin juya halin sauyin dimokuraɗiyya (NMFDC), da sauran ƙarin wasu ƙungiyoyi ne suka nemi shugaban EFCC ya sauka.

Ƙungiyoyin, masu fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa sun buƙaci shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa da ya sauka daga kujerarsa saboda a bincikesa kan zargin cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Kungiya Ta Gabatarwa Tinubu Aikin Farko Da Ta Ke Son Ya Yi Da Zarar Ya Shiga Ofis

Wasu kungiyoyi sun nemi shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa ya yi murabus
Wasu kungiyoyi sun nemi shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa ya yi murabus. Hoto: Peoples Gazette
Asali: UGC

Kungiyoyin sun kuma buƙaci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da ya ba da fifiko kan al’amuran cin hanci da rashawa, inda suka jaddada cewa, wannan abu ne da ya shafi kowa ba tare da la’akari da matsayin mutum ba.

Kiran dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetocin ƙungiyoyin da suka haɗa da Israel Uwejeyan, Bello Idowu da Mustapha Musa, kamar yadda Guardian ta wallafa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun zargi Bawa da rashawa da kuma bita da ƙulli

Ƙungiyoyin sun ce bai kamata a samu wata hukuma ta gwamnati da ke hukunta masu laifi da nuna wariya ba wajen gudanar da hukunci.

Sun kuma ce bai kamata hukumar ta EFCC ta riƙa yi wa mutane bita da ƙulli ba a yayin da suka gaza magance matsalolin zarge-zargen cin hanci da ake musu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Wa Obasanjo Wankin Babban Bargo, Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu Da Ya Kasa Yi Wanda Buhari Ya Yi

Ƙungiyoyin sun kuma ce yadda ake yi a ko ina faɗin duniyar nan shi ne, duk wani jami'i da ake gudanar da bincike a kansa, to dole ne ya sauka daga kan muƙaminsa har a kammala bincike.

Mutane na da hujjoji kan zargin nasu

Haka nan sun yi iƙirarin cewa mutane da dama na da hujjoji da suke da su na tuhumar shugaban na EFCC Abdulrasheed Bawa kan laifukan cin hanci da rashawa.

A cewarsu:

“Kamar yadda kowace hukuma ta gwamnati take a ko ina, akwai ka’idojin aiki da jami’ai ke bi, waɗanda ake zarginsu da aikata laifuka, su sauka daga kan muƙamansu, a yayin da aka gudanar da bincike don tabbatar da gaskiyar tuhumar da ake musu.”
“Wasu manyan mutane a Najeriya da dama sun yi iƙirarin cewa suna da hujjoji na cin hanci da rashawa, da cin amanar jama’a da kuma cin zarafin ofishin EFCC da suke zargin shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa.”

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Zo da Sabon Tsari, Ya Umarci Kwamishinoni da Hadimai Su Bayyana Dukiyarsu, Ya Kore Su

Sun buƙaci a tsige Abdulrasheed Bawa

Ƙungiyoyin sun ce da waɗannan hujjoji ne suka dogara, sannan suke kira ga shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya sauka daga muƙaminsa kuma ya mika wuya domin bincike.

Sun kuma ce idan Bawa ya yi kunnen uwar shegu da wannan kira nasu, suna roƙon da a sauke shi daga muƙaminsa, sannan a yi masa kamar yadda aka yi wa Ibrahim Magu.

A kalamansu:

“Muna buƙatar idan Bawa ya ƙi ya sauka, a kore shi, sannan a yi masa bincike mai tsanani, kamar yadda aka yi wa magabacinsa Ibrahim Magu.”

Sai dai a wani rahoto na PM News, kungiyar marubuta da ke fafutukar kare hakkokin dan adam ta Najeriya (HURIWA), ta caccaki duk masu kiraye-kirayen cewa a cire Bawa daga mukamin nasa.

EFCC za ta binciki gwamnoni 28

A wani labarin namu na baya, kun karanta cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) za su binciki gwamnonin Najeriya guda 28.

Gwamnonin da za a bincika dai sun haɗa da waɗanda za su kammala wa'adin mulkinsu a ranar 29 ga watan Mayu, waɗanda suka yi wa'adi ɗaya kacal da kuma wasu da za su koma a zagaye na biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel