Gwamnan Legas Ya Umarci Kwamishinoni Su Faɗi Abinda Suka Tara Kan Su Sauka

Gwamnan Legas Ya Umarci Kwamishinoni Su Faɗi Abinda Suka Tara Kan Su Sauka

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya umarci kwamishinoni su faɗi yawan dukiyarsu gabanin su miƙa mulki daga nan zuwa ranar Jumu'a
  • Hakan na ƙunshe a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ma'aikatan jihar Legas, Muri Okunola
  • Gwamnan ya gode wa kwamishinonin da baki ɗaya hadimansa bisa gudummuwar da suka bayar

Lagos - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya umarci masu rike da muƙaman siyasa su bayyana adadin dukiyarsu yayin miƙa ragamar mulkin ma'aikatun da suka riƙe.

Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan ya buƙaci dukkan mambobin majalisar zartarwa su tabbata sun miƙa mulki daga yau zuwa ranar Jumu'a 26 ga watan Mayu, 2023.

Gwamna Sanwo-Olu.
Gwamnan Legas Ya Umarci Kwamishinoni Su Faɗi Abinda Suka Tara Kan Su Sauka Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Facebook

Ya ce sharaɗin da ya kafa musu na bayyana dukiya gabanin sauka daga kan kujerunsu ya yi daidai tanadin dokar kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

29 Ga Mayu: Gwamnoni 5 Masu Barin Gado Wadanda Mai Yiwuwa Ba Za Su Miƙa Mulki Cikin Ruwan Sanyi Ba Da Dalilai

Sanwo-Olu ya ba da wannan umarnin ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ma'aikatan jihar Legas, Muri Okunola.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Waɗanda umarnin gwamna ya shafa

Ya ƙara da bayanin cewa waɗanda matakin ya shafa sun haɗa da kwamishinoni, dukkan mashawarta na musamman, mataimaka na musamman da baki ɗaya hadiman gwamna.

Haka nan Gwamna Sanwo-Olu ya buƙaci kowane ɗaya daga cikinsu ya shirya bayanan miƙa mulki kuma su miƙa kadarorin gwamnati ciki harda motoci ga babban ma'aikaci a wuraren da suka jagoranta.

Sanarwan ta ce:

"Wannan umarni bai shafi shugabannin hukumomi da majalisar gudanarwan wasu hukumomi, waɗan da doka ta tanadar musu wa'adi ba matuƙar ba sun samu bayani a hukumance ba."

Daga ƙarshe, gwamnan ya gode wa baki ɗaya hadiman bisa gudummuwar da suka baiwa gwamnatinsa kana ya musu fatan alheri kan al'amuran da zasu ta sa nan gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ta Kori Kwamishinoni da Hadimansa Daga Aiki, Ya Ba Su Bsbban Umarni

A ranar Litinin mai zuwa za'a rantsar da Gwamna Sanwo-Olu karo na biyu bayan lashe zaben gwamna ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Gwamnan Gombe ya gaji Lalong a ƙungiyar NGF

A wani labarin kuma Gwamna Inuwa Yahaya Ya Samu Nasarar Zama Shugaban Gwamnonin Arewa.

Gwamnonin arewacin Najeriya sun zabi takwaransu na jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, a matsayin sabon shugaban ƙunguyar NGF.

Asali: Legit.ng

Online view pixel