“Albashina N75k Ne”: Matashiya Ta Kai Karar Mijinta Gaban Iyayenta Saboda Ya Bata N30k

“Albashina N75k Ne”: Matashiya Ta Kai Karar Mijinta Gaban Iyayenta Saboda Ya Bata N30k

  • Wata matar aure na bakin ciki ganin cewa mijinta ya bata N30,000 ne kacal don kula da kanta da ragamar gida
  • Tana neman ayi mata kari, amma mijin nata ya ce N75,000 ne albashinsa duk wata kuma ba zai iya yi mata kari ba
  • Mutumin ya ce bayan N30,000 da yake ba matar tasa duk wata, yana kuma biyan kudin makarantar yaransa da sauransu

Wata matar aure ta kira mijinta da kankamo saboda ya bata N30,000 kacal a matsayin kudin kayan abinci.

A wani sakon sirri da ya aikewa @jon_d_doe, mijin matar ya koka cewa matarsa bata farin ciki da yanayin yadda yake tafiyar da harkokin iyalinsa ta fuskacin kudi.

Matashiya, kudi da matashi
“Albashina N75k Ne”: Matashiya Ta Kai Karar Mijinta Gaban Iyayenta Saboda Ya Bata N30k Hoto: Getty Images/Vladimir Vladimirov, Bloomberg and Westend61
Asali: Getty Images

Mutumin ya ce N75,000 yake dauka a matsayin albashi duk wata. Daga cikin wannan kudin, yana baiwa matarsa N30,000 don kula da harkokin gida.

Kara karanta wannan

Ni Mutum Ne Mai Saurin Fushi, In Ji Gwamna Babagana Zulum

Matar aure ta yi karar mijinta gaban iyayenta saboda kudi

Yana kuma biyan kudin makarantar yaransa su uku, wanda ya kai kimanin N90,000 duk zangon karatu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, sam hakan bai yi matar tasa ba kuma ta kai lamarin gaban iyayenta. Ta fada ma iyayenta cewa mutumin kankamo ne kuma baya kula da iyalinsa.

Ya rubuta:

"Matata tana rigima da ni, kuma ta fada ma iyayenta cewa ni kankamo ne kuma cewa bana kula da su."

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

@dhan_ddirectorh ya ce:

"Ko ni da bani da aure 80k baya isata duk wata balle a kai ga mai yara uku da mata yana daukar 75k ahhhh."

@Thegreenivy_ ta ce:

"Da alama matar ma bata da kudaden shiga. Ta yaya za ka yi malejin 75k a wannan tattalin arziki baaba ya kamata matar ta tashi ta nemi na kai ita ma ta dunga kawo wani abu gida. Baaba 75k kan mutum 5."

Kara karanta wannan

Matashi Ya Girgiza Bayan Budurwarsa Ta Nemi Ya Kawo N12m Domin Bikin Aurensu, Ya Dauki Mataki Mai Tsauri

@onyeama_joseph ya ce:

"Ina fadi a kodayaushe ya kamata maza su dunga duba aljihunsu kafin su hayayyafa."

Bidiyon wasu kyawawan yan mata da ke aiki a kamfanin biskit ya dauka hankali

A wani labarin kuma, mun ji cewa jama'a a shafukan soshiyal midiya sun jinjinawa wasu yan mata kan yadda suka dage don neman na dogaro da kai.

Wani bidiyo da ya yadu a intanet ya nuno kyawawan yan matan suna aiki tukuru a wani kamfanin yin biskit.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel