“Aikin Nan Ba Sauki”: Kyawawan Yan Najeriya Sun Nuna Kwarewarsu a Kamfanin Yin Biskit

“Aikin Nan Ba Sauki”: Kyawawan Yan Najeriya Sun Nuna Kwarewarsu a Kamfanin Yin Biskit

  • Bidiyon wasu kyawawan yan mata yan Najeriya da ke aiki tukuru kamar injina a wani kamfanin yin biskit ya burge mutane da dama
  • Bidiyon da ya yadu a Instagram ya nuno yan matan suna dauka tare da shirya biskit cikin sauri
  • Masu amfani da soshiyal midiya da suka ga bidiyon sun yaba ma yan mata a kan aikin da suke yi don dogaro da kai

Wani dan gajeren bidiyo na wasu yan Najeriya da ke aiki a wani kamfanin biskit ya bayyana a soshiyal midiya.

Bidiyon ya nuno wasu yan mata biyu masu kwazon aiki suna shirya biskit cikin sauri kamar wasu inji.

Yan mata a kamfanin yin biskit
“Aikin Nan Ba Sauki”: Kyawawan Yan Najeriya Sun Nuna Kwarewarsu a Kamfanin Yin Biskit Hoto: @saintavenue_ent
Asali: Instagram

Suna ta daukar biskit din sannan suna jera su a cikin wani kwali cikin sauri yayin da suke hira da raha a tsakaninsu.

Saurin hannayensu ya kara kawatar da aikin wanda ke nuna kamar yana da sauki sannan mutane sun yaba ma jajircewarsu.

Kara karanta wannan

Inda Ranka: Jama'a Sun Sha Kallo Yayin da Wani Mutum Ya Fito Da Motarsa Mai Siffar Takalmi Yana Tuka Ta a Biti, Bidiyon Ya Yadu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar wasu mutane, watakila suna fama da ciwon jiki bayan aikin. Wasu kuma sun bayyana cewa irin wadannan mata masu kwazon nema su ya kamata a dunga ganowa da kuma taimaka masu.

Jama'a sun yi martani

@Dwise_d ta ce:

"Wadannan ne matan da suka cancanci a kashewa kudi."

@Okeke__Kingsley ta ce:

"Irin wadannan ma'aikatan nake bukata a shaguna na."

@hexlord001 ta yi martani:

"Neman na sakawa a bakin salati ba abu ne mai sauki ba."

@royal_dir ta yi martani:

"Irin wadannan yan matan ne zan iya ba 2k na gaggawa."

@_bullettv ta ce:

"Abun takaici shine ba za su biya su sama da 30k duk wata ba."

@youngest_ucf ya yi martani:

"Wadannan ba karamin kudi suke samu ba a kasar waje fa."

@c_namani ya ce:

"Fafutukar yau da kullun ya zama fasaha."

Kara karanta wannan

Matar Aure ta Sha Suka Bayan Ta Boye Fuskar Mijinta a Hotunan Shakatawa Da Suka Fita

Kalli bidiyon a kasa:

Matashiya ta gwangwaje kanta da dan karamin gida

A wani labarin kuma, wata matashiya ta cika da farin ciki bayan ta tara yan kudadenta sannan ta kerawa kanta dan karamin gida domin ta samu saukin biyan kudin haya.

Matashiyar ta ce koda dai gidan bai da girka kamar sauran gidaje tana farin ciki kuma ta mallaki muhallin da za ta kira nata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel