Matashi Ya Girgiza Bayan Budurwarsa Ta Nemi Ya Kawo N12m Domin Bikin Aurensu, Ya Ce Ya Fasa

Matashi Ya Girgiza Bayan Budurwarsa Ta Nemi Ya Kawo N12m Domin Bikin Aurensu, Ya Ce Ya Fasa

  • Wani matashi ɗan Najeriya ya koka a soshiyal midiya bayan budurwarsa ta nemi ya kawo sama da N10m domin aurensu
  • A cikin sautin murya da ya saki a soshiyal midiya, budurwar ta sa ta gaya masa cewa an gaya mata cewa komai da komai na bikinsu zai lashe fiye da N10m
  • Hakan ya fusata matashin, inda ya tambayeta cewa ko iyayenta sun kashe waɗannan maƙudan kuɗin lokacin bikin aurensu

Wani matashi ɗan Najeriya ya soke bikin aurensa da wacce zai aura bayan ta bayyana kuɗin da za a kashe a bikin.

Budurwar a cikin wani sautin murya da ta turawa saurayin na ta, ta bayyana cewa bikin auren na su zai laƙume tsakanin N10m zuwa N12m.

Budurwa ta nemi saurayinta ya kawo N12m domin shagalin biki
Matashin ya fusata bayan ta nemi ya N12m Hoto: @Uriel Sinai, Igor Alexsander/ Getty Images, Instablog9ja/Instagram
Asali: UGC

A kalamanta:

"Dangane da bikin aurenmu, na tambayi wata kan shirye-shiryen biki, inda tace ana buƙatar N2.5m a shirya bikin. Kwalliyar wajen biki N1.5m. Dangane da mai dafa abinci, yana neman N2.5m."

Kara karanta wannan

"Dole Sai Yana Samun N3m": Budurwa Mai Samun N3.7m a Wata Ta Bayyana Irin Mijin Da Ta Ke Son Yin Wuff Da Shi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sannan sai maganar kek, wannan mai ɗan karen kyawun nan mai hawa biyar. Suna cewa zai kai N5m. Duka idan aka haɗa zai kama wajen N10m zuwa N12m. Rabin raina ka min magana idan ka ga saƙona."

Martanin matashin mai son aure

Da ya ke mayar mata da martani, matashin ya fusata inda ya tambaye ta, ko iyayenta sun kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗen lokacin bikin aurensu. Ya kuma ƙara da cewa ya fasa auren.

A kalamansa:

"Wai duk waɗannan abubuwan da kike magana akai, na yin kwalliya ne kawai da kek. Ba damuwa. Lokacin da babanki zai auri mahaifiyarki ba su yi kek ba. Basu kira mai dafa abinci ba. Na fasa saboda wannan shirmen da kika gayamin."

Ƴan soshiyal midiya sun yi tsokaci

Thevanesaonly ta rubuta:

"Idan dai har yana da kuɗin, to menene abin tayar da jijiyar wuya don ka kashe kuɗi kan abinda kake so."

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Jiga-Jigan Jam'iyyun Adawa Da Tinubu Zai Naɗa Bayan Rantsarwa

_omote ya rubuta:

"Ka yi amfani da N5m ɗin kek ka je makaranta. Makarantar kuɗi fa kada matsalar ASUU ta shafe ka."

Budurwa Mai Samun N3.7m a Wata Ta Bayyana Irin Mijin Da Ta Ke Son Yin Wuff Da Shi

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa mai neman mijin da za ta aura, ta bayyana irin abubuwan da ta ke so ta samu a tattare da wanda ya ke sha'awar aurenta.

Budurwar wacce ta ke samun N3.7m a wata, ta bayyana cewa dole ne ya kasance wanda zai aureta yana da hanyar samun kuɗi, wacce kowane wata za ta iya samar masa da N3m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel