Farfesa Isa Pantami Ya Fara Shirye-Shiryen Sauka Daga Kujerar Ministan Sadarwa, Bayanai Sun Fito
- Ministan ma'aikatar sadarwa da tattalin arziƙin zamani ta ƙasa, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami ya fara shirye-shiryen kwashe kayansa daga ma'aikatar
- Pantami ya bi sahun wasu daga cikin ministocin da suka fara kwashe kayayyakinsu daga ofis gabanin ranar 29 ga watan Mayu da za a rantsar da sabuwar gwamnati
- Ministocin dai na hannanta ayyukan ma'aikatun da suke jagoranta ne ga manyan sakatarorin dindindin na ma'aikatun
Abuja - A cikin kwanakin da suka rage na shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kammala wa'adinsa, ministoci sun fara miƙawa manyan sakatarorin dindindin na ma’aikatunsu kujerunsu gabanin rushe majalisar ministocin.
A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu 2023, wa'adin mulkin shugaba Buhari na shekaru takwas, wanda ya fara daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa yau zai zo ƙarshe.

Asali: Facebook
Pantami ya aiwatar da aikinsa na ƙarshe a makon da ya gabata
Ministan ma'aikatar sadarwa da tattalin arziƙi, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya gudanar da aikinsa na kusa da ƙarshe a makon da ya gabata lokacin da ya kaddamar da wani kwamiti kan kuɗaɗen yanar gizo (blockchain) a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan ma yau Laraba, ministan ya wakilci shugaban ƙasa wajen wani taron ci-gaban tattalin arziƙi da aka gudanar a ma'aikatar kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Fesbuk.
Kamar yadda wasu ministocin suka fara shirye-shiryen barin ofis, alamu na nuni da cewa shima ministan sadarwar ya fara haɗa kayansa don barin ofis.
Daily Trust ta ce wani da ke aiki a ma'aikatar sadarwa ta ƙasa, ya bayyana cewa ya ga ma'aikatan ofishin ministan na kwashe takardu da wasu kayayyakinsa daga ofis a ranar Litinin ɗin da ta gabata.
Minista ya bada umarnin a rushe kasuwar UTC
Sai dai shi a nasa ɓangaren, ministan babban birnin tarayya, Malam Muhammad Bello, ya bayar da umarnin rusa shaguna a babbar kasuwar UTC da ke Area 10, da kuma wasu gidaje a Gishiri da dai sauransu.
An ce har yanzu dai ministan yana zuwa ofis domin aiwatar da wasu ayyuka a hukumance.
Buhari ya naɗa sabbin muƙamai a ƙasa da kwana bakwai kafin rantsuwa
A wani labarin na daban kuma, shugaba mai barin gado Muhammadu Buhari ya naɗa wasu sabbin muƙamai guda shida, duk da yana a satin ƙarshe na wa'adinsa.
Daga cikin waɗanda aka naɗa a sabbin muƙamai akwai dakta Steven Andzenge da aka bai wa shugabancin NDPHCL.
Asali: Legit.ng