Yanzu Yanzu: Rigima Ta Kaure Tsakanin Gbajabiamila Da Wase a Zauren Majalisa

Yanzu Yanzu: Rigima Ta Kaure Tsakanin Gbajabiamila Da Wase a Zauren Majalisa

  • Rigima ta kaure tsakanin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da mataimakinsa, Idris Wase
  • Lamarin ya samo asali ne lokacin da Gbajabiamila ya bukaci a takaita harkokin majalisar na ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu saboda kaddamar da hedkwatar NILDS
  • Wase ya nuna adawa ga wannan bukata ta shugaban majalisar cewa taron bai kai da za a takaita zaman majalisar saboda shi ba

Abuja - Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da mataimakinsa sun yi karo a bainar jama'a yayin zaman majalisa a ranar Laraba, 24 ga watan Mayu kan wata sanarwa da shugaban majalisar ya yi game da takardar oda na ranar Alhamis.

Gbajabiamila dai ya bukaci a takaita takardar domin ba yan majalisar damar halartan taron kaddamar da Cibiyar Nazarin Dimokradiyya da Dokoki ta kasa (NILDS), jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Lissafi Zai Koma Sabo a APC, Ahmad Lawan Zai Iya Shiga Takarar Majalisar Dattawa

Gbajabiamila and Wase
Yanzu Yanzu: Rigima Ta Kaure Tsakanin Gbajabiamila Da Wase a Zauren Majalisa Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

An yi cacar baki tsakanin Gbajabiamila da Wase

Kafin dage zaman majalisar, kakakin majalisar ya sanar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da cibiyar NILDS tare da hanyar filin jirgin sama da misalin karfe 3:00pm na ranar Alhamis.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bukaci shugaban kwamitin majalisa kan Tsare-tsare da harkoki da ya tabbatar da ganin cewa takardar oda bata yi karo da tsare-tsaren ranar ba don majalisar ta dage zamanta da wuri saboda taron.

Sai dai kuma, mataimakin kakakin majalisar, Idris Wase ya ce babban aikin majalisar shine aiwatar da doka da sauran harkoki da yake na hukuma, yana mai cewa kaddamar da hedkwatar NILDS bai isa dalili na dage zaman majalisar ba.

Wase ya ce yan majalisa da ke son halartan taron na iya aikata hakan ba tare da kawo karan tsaye ga harkokin majalisar ba, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sa Hannu, Ya Kawo Dokoki 8 a Makon Karshensa a Ofis

Sai dai kakakin majalisar ya ce: "Ya mataimakin kakakin majalisa, watakila ba ka fahimci muhimmancin NILDS ba kamar yadda wasunmu suka fahimta. Ba wai za mu dage zaman majalisar don yan majalisa su halarci kaddamar da cibiyar bane. Cewa na yi a takaita takardar oda saboda zan halarci bikin kaddamarwar."

Sai dai kuma Wase ya mayar masa da martani cewa: "Ya kakakin majalisa, majalisar ba kan karan kaina bane, sai dai mu."

Da farko Gbajabiamila ya share mataimakinsa, ya yi sabuwar sanarwa kafin ya koma gare shi yana mai cewa: "Mataimakin kakakin majalisa, na kasance a majalisar nan da ya kai na san cewa wannan shine karo na farko a tarihin majalisar nan da mataimakin kakakin majalisa zai fito karara ya nuna adawa da abun da kakakin majalisa ya fadi."

Da ya juya ga shugaban kwamitin majalisa kan tsare-tsare da harkoki, Gbajabiamila ya ce: "ka takaita takardar gobe. Zauren nan zai tashi da karfe 2:00 na rana" yayin da yan majalisar da suka hallara suka amsa kuwa.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Yadda ’Yan Majalisu Ke Raba Daloli Don Neman Goyon Bayan a Zabe Su

Abun da ya kawo rabuwan kai tsakanin Gbajabiamila da Wase

Lamuncewa Hon. Tajudeen Abbas a matsayin kakakin majalisa ta 10 ya haifar da rabuwan kai tsakanin kakakin majalisar da mataimakinsa.

An tattaro cewa Wase ya kauracewa halartar taron shugabanni da aka saba yi kafin zaman majalisar na yau da kullum, inda ya ke kuma kaucewa tattakin da kakakin majalisar kan yi zuwa zauren majalisar.

Ya fito karara ya zargi kakakin majalisar da marawa Tajudeen baya don darewa kujerar kakakin majalisar.

Ba na zawarcin kowace kujera a gwamnatin Tinubu, El-Rufai

A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya karyata rade-radin cewa yana kamun kafa domin samun mukamin shugaban ma'aikatan shugaban kasa a majlisar Bola Tinubu.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a Gombe a ranar Asabar, 6 ga watan Mayu yayin da yake jawabi ga manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel