Daga Karshe: Buhari Ya Sauka a Jihar Lagos Don Kaddamar da Matatar Mai Ta Dangote

Daga Karshe: Buhari Ya Sauka a Jihar Lagos Don Kaddamar da Matatar Mai Ta Dangote

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Lagos don kaddamar da matatar mai ta Aliko Dangote a jihar
  • Buhari ya samu tarba daga gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu da kuma Alhaji Aliko Dangote da kansa
  • Aliko Dangote ya godewa shugaba Buhari da kuma zababben shugaban kasa, Tinubu bisa taimako da suka bayar

Jihar Lagos - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Lagos don kaddamar da matatar mai ta shahararren dan kasuwa Aliko Dangote.

Matatar wadda ta ke Ibeju-Lekki a jihar Lagos za ta fara fitar da akalla litar man fetur miliyan 38 da bakin mai da kuma man a jiragen sama a kullum.

Buhari ya sauka a jihar Lagos
Buhari Ya Sauka a Jihar Lagos Don Kaddamar da Matatar Mai. Hoto: Punch
Asali: Facebook

Sannan matatar a kullum za ta fitar da ganga 650,000 na danyen mai wadda za a sarrafa shi zuwa man fetur da kalanzir da gas da kuma mai na jiragen sama.

Kara karanta wannan

Bayan Haduwa da Tinubu a Kasar Waje, Kwankwaso da Abba Sun Dura Garin Legas

Buhari ya samu tarbar manya

Punch ta tattaro cewa shugaba Buhari ya samu tarba daga gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu da kuma shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana tsammanin shugabannin kasashe da dama za su halarci bikin kaddamarwar wadanda suka hada da shugaban kasar Togo, Gnassingbe Eyadema, da takwaransa na Ghana, Nana Akufo-Addo da na Senegal Macky Sall.

Sauran sun hada da shugaban kasar Niger, Mohammed Bazoum da takwaransa na kasar Chadi, Mahamat Deby.

Dangote ya yaba wa Buhari

Gidan talabijin na Channels ta tattaro cewa a yayin bikin, shugaban matatar, Aliko Dangote ya godewa shugaba Buhari da kuma zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa gudumawar da suka bayar don ganin matatar ta tsaya da kafafun ta.

Dangote wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter ya yabawa shugaba Buhari da sauran ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suke bai wa kamfaninsa tun daga farko har zuwa lokacin da aka kammala matatar.

Kara karanta wannan

Yadda Daura ke Shirin Tarbar Shugaba Buhari Bayan Bayajidda II Ya Sauka Daga Mulki

“Ina so na mika godiya ta ga ‘yan Najeriya saboda goyon baya da suke ba wa kamfaninmu na Dangote, da kuma taimako da muka samu daga shugaba Buhari da gwamnatinsa, sannan zababben shugaban kasa da ya samar da matattarar kasuwanci ta Lekki.
“Har ila yau ina mika godiya ga gwamnonin jihar Lagos kamar su Fashola da Ambode da kuma gwamna mai ci Babajide Sanwo-Olu dukkansu sun bamu gudumawar da muke bukata.”

Matatar an Dangote: Dalilin Da Ya Sa Muka Shiga Harkar Mai, in ji Dangote

A wani labarin, shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilansa na shiga harkan mai.

Dangote ya yi bayani dalla-dalla akan abubuwan da suka ja hankalinsa zuwa harkan mai a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel