Majalisar Dattawan Najeriya Ta Taya Ike Ikweremadu Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Taya Ike Ikweremadu Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

  • Majalisar dattawan Najeriya ta tuna da tsohon mataimakin shugabanta, Ike Ikweremadu a ranar haihuwarsa
  • Shugaban majalisar shine ya taya Ekweremadu murnar zagayowar ranar haihuwarsa a zaman majalisar na ranar Talata
  • Ekweremadu dai yana can tsare a UK bayan kotu ta same shi da laifin safarar sassan jikin ɗan adam

Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta taya tsohon mataimakin shugabanta, Ike Ikweremadu, wanda ya ke garƙame a gidan gyaran hali a UK, murnar cikarsa shekara 61 a duniya.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa, shugaban majalisar dattawan, sanata Ahmed Lawan shine ya sanar da zagayowar ranar haihuwar Ekweremadu, a zaman majalisar na ranar Talata.

Majalisar dattawa ta taya Ikweremadu murnar zagayowar ranar haihuwarsa
Sanata Ike Ikweremadu Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Ike Ekweremadu shine ya ke wakiltar Enugu ta Yamma a majalisar dattawan ta yanzu.

Wata kotun majistare a Westminster, ta samu Ikweremadu, matarsa Beatrice sa wani likita mai suna Obinna Obetta, ta haɗa baki wajen yin safarar sassan jikin ɗan adam, laifin da ya saɓawa sabuwar dokar hana bauta ta wannan zamanin.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Takarar Akpabio Da Barau Ta Samu Tagomashi, Wasu Jiga-Jigan Jam'iyyar APC Sun Mara Mu Su Baya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai shari'a Johnson ya yankewa Ekweremadu, hukuncin shekara tara da wata takwas a gidan gyaran hali, matarsa hukuncin shekara huɗu da wata shida, yayin da aka yankewa Obetta hukuncin shekara 10 a gidan kaso.

Majalisar ta tuna da tsohon mataimakin shugabanta

Sai dai, a zaman majalisar na ranar Talata, shugaban majalisar ya yi addu'ar Allah ga ƙarawa Ikweremadu tsawancin kwana da rayuwa mai albarka, cewar rahoton Gazettengr.

Ike Ekweremadu dai ya zo duniyar nan ne a ranar 12 ga watan Mayun 1962, inda yanzu ya ke da shekara 61 da haihuwa a duniya.

Ekweremadu Da Sauran Jerin Manyan 'Yan Siyasar Da Aka Taba Kullewa a Kasar Waje

A wani rahoton na daban kuma, mun kawo mu ku jerin ƴan siyasan Najeriya da aka taɓa garƙamewa a ƙasashen waje, saboda aikata laifuka daban-daban.

Kara karanta wannan

Daga Buhari Zuwa Dogara: Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisar Wakilai Tun 1999 Zuwa Yanzu

Ike Ikweremadu wanda kotu ta yankewa hukuncin shekara tara da watanni a UK, yana daga cikin jerin ƴan siyasan ƙasar nan da aka taɓa turawa gidan kaso a ƙasar waje.

Ikeweremadu ba shine na farko ba a cikin ƴan siyasar ƙasar nan da aka taɓa sakayawa a gida gyaran hali a ƙasashen waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel