Yanzu-Yanzu: An Kara Kudin Aikin Hajjin Bana Na Shekarar 2023

Yanzu-Yanzu: An Kara Kudin Aikin Hajjin Bana Na Shekarar 2023

  • Hukumar jindaɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON), ta sanar da yin ƙari kan kuɗin aikin hajjin bana na shekarar 2023
  • Hukumar tace ƙarin ya biyo bayan neman yin ƙari kan kuɗin aikin hajjin da kamfaanonin jiragen sama na nan gida Najeriya suka yi ne
  • Shugaban hukumar ya bayyana cewa ƙarin ba zai shafi maniyyata, hukumar ce za ta ɗauki nauyin alhakin biya

Abuja - Hukumar jindaɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa kamfanonin jiragen sama guda huɗu na ƙasar nan, sun buƙaci da a ƙara kuɗin hajjin bana na shekarar 2023.

Shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan, ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sun buƙaci da a ƙara kuɗin da $250, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

An kara kudin aikin hajjin bana na 2023
Hukumar NAHCON, ta kara kudin hajjin bana Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa kamfanonin jiragen su ne, Air Peace, Azman, Max Air da Aero Contractors. Dalilin su na neman ƙarin ya ginu ne akan rikicin da ake yi a ƙasar Sudan, wanda zai sanya sai sun bi doguwar hanya kafin su isa ƙasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnoni Masu Barin Gado Da Za Su Bar Magadansu Da Biyan Bashin Albashin Ma'aikata

Da ya ke magana a birnin tarayya Abuja, wajen horar da jami'an hukumar na jihohi a ranar Asabar, Hassan ya bayar da tabbacin cewa maniyyatan ba za su biya ko sisi ba a dalilin ƙarin, cewar rahoton The Cable.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Kamfanonin jiragen saman mu na nan gida Najeriya sun yarda da ƙarin $250 kan kuɗin jirgi na wannan shekarar. Mu na duba hanyoyin da za mu magance wannan ƙarin da aka samu."
"Mu na cigaba da addu'ar Allah ya kawo mafita kan wannan rikicin na Sudan ta yadda za a buɗe sararin samaniyar su da kuma kawo ƙarshen kashen-kashen ba gaira ba dalili da ake na mutanen Sudan"
"Mu a nan a hukumar NAHCON, mu na duba dukkanin hanyoyin da za mu bi domin ɗauke wannan ƙarin da aka samu. Mun cimma matsaya cewa duk matakin da za mu ɗauka, ba zai buƙaci maniyyata su ƙara biyan wasu kuɗi ba ga hukumomin Alhazai na jihohin su. Ba su buƙatar ƙara biyan wasu kuɗi."

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalili 1 Rak da Yasa Tinubu da APC Suka Zabi Akpabio da Abbas, Shettima Ya Tona Gaskiya

Ya kuma ƙara da cewa hukumar ta sanya ranar 25 ga watan Mayu, a matsayin ranar fara jigilar maniyyatan bana zuwa ƙasa mai tsarki

Da Alamu Za A Ƙara Wa Mahajjatan Bana Na Najeriya Kuɗin Jirgi

A baya mun kawo rahoto kan yiwuwar ƙara wa mahajjatan bana kuɗin jirgi a Najeriya, saboda rikicin da ake tafka wa a ƙasar Sudan.

Yiwuwar ƙarin na zuwa ne duba da wahalar da kamfanonin jiragen sama za su sha, wajen jigilar maniyyatan bana zuwa ƙasa mai tsarki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel