"Ta Wakilce Mu”: ’Yar Najeriya Ta Fasa Taro da Kwalliyan da Ba a Taba Gani Ba a Bikin Nada Sarki Charles

"Ta Wakilce Mu”: ’Yar Najeriya Ta Fasa Taro da Kwalliyan da Ba a Taba Gani Ba a Bikin Nada Sarki Charles

  • Wata mata ‘yar Najeriya ta ba da mamaki yayin da ta dura a Westminster Abbey a lokacin bikin rantsar da sarki Charles III
  • Matar mai suna Eva Omoghomi ta sanya sutura ce irin ta al’adar yarbawa ga kuma wani gele da ya hau ya zauna a jikinta
  • Jama’ar kafar sada zumunta sun shiga mamaki, inda suka yi martanin yaba mata bisa wakiltar Najeriya da al’adarta

Wata mata ‘yar Najeriya ta ba da mamaki yayin da ta wakilci al’adar kasar nan a birnin Landan yayin bikin nadin sarautar sarki Charles III da matarsa Camila.

Matar ta dura Westmintser Abbey sanye da sutura irinta Yarbawa da kuma wani gele da ya tafi daidai da launin suturar da ta santa.

Suturar dai da ta sanya ya sanya ta fasa taro, domin idon jama’a ya koma kanta yayin da ake hidimar bikin sarautar.

Kara karanta wannan

Turai ‘Yar’adua Ta Tuna da Lokacin Karshe da Marigayi Shugaba ‘Yar’adua a Aso Rock

Mata ta fasa taro a Ingila
Hotunan matar da ta fasa taro a Ingila | Hoto: @channelstelevision
Asali: Instagram

‘Yar Najeriya ta fita daban a taron nada sarki Charles III

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar mai suna Eva Omaghomi ta kasance ma’aikaciyar sarkin, kuma ta bayyana a wurin taron da aka yi a yau Asabar 6 ga watan Mayu ba kamar sauran jama’aba.

‘Yan Najeriya a kafar sada zumunta sun yi mamaki, inda suka bayyana annashuwa game da ganin an mutunta al’adar gida.

Dan jaridar AFP, Paul Ellis ne ya dauki hotunan, inda kafar labaran Channles Tv ta yada su a Instagram.

Kalli hotunan:

Martanin jama’a

@urenmanaturals:

“Ta ba da mamaki kuma ta nuna kasaita!!!.”

@likavogue:

“Ta yi matukar kyau. Salon tufar Afrika akwai kasaita.”

@jennyfromdblocc:

“Kuma ta fita daban.”

@bindeys_effect:

“Ta wakilce mu yadda ya kamata.”

@andersonainsta:

“Duk wanda ka gani a nan bako ne da ya rufe jikinsa. Maza da mata masu mutunci.”

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Cafke Matashi Da Ya Halaka Mahaifiyarsa a Kano

@d_nugos:

“Najeriya ko dai babu. Fitacciya kuma ta daban.....duk wadannan ‘yan kwalliyan idanunsu zai bude.”

Shugaba Buhari ya tafi bikin nada sarki Charles

A wani labarin, kunji yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tattaki zuwa kasar Ingila domin halartar bikin nadin sarautar sarki Charles na III.

Shugaban kasan ya yi tafiyar ne a daidai lokacin da ya rage masa kwanaki kadan ya sauka daga mulkin kasar nan a karshen Mayu.

Idan baku manta ba, Allah ya yiwa sarauniyar Ingila rasuwa, inda aka ayyana danta Charles a matsayin sabon sarki a 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel