Buhari Zai Shilla Ingila Don Halartar Nadin Sarautar Sarki Charles

Buhari Zai Shilla Ingila Don Halartar Nadin Sarautar Sarki Charles

  • Shugaba Buhari zai tafi kasar Burtaniya a yau dinnan don halartar bikin nadin sarautar sarki Charles na uku
  • Shugaban zai samu rakiyar manyan kusoshin gwamnatinsa da suka hada da sakataren gwamnatin tarayya
  • Kakakin shugaban, Femi Adesina ne ya fitar da wannan inda ya bayyana dalilin ziyarar da sauran tarurrukan da Buhari zai halarta

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Landan a yau dinnan domin halartar bikin sarautar Sarki Charles na uku da matarsa sarauniya Camila.

Shugaban zai samu rakiyar jiga-jigan gwamnatinsa da suka hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyema da ministan yada labarai, Lai Mohammed.

Charles da Buhari
Sarki Charles na Ingila tare da Shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran sun hada da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Babagana Munguno da darakta na hukumar leken asiri ta kasa, Ambasada Ahmed Rufaì da sauran kusoshin gwamnati, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Fadawa Bola Tinubu Alfarmar da Yake Nema a Wajen Gwamnatinsa

Shugaba Buhari kan yi tafiya irin wanna, inda yake daukar manyan jiga-jigan gwamnati ya tafi dasu kasashen waje.

Yaushe za a yi nadin sarautar?

Kakakin shugaban kasan, Mista Femi Adesina a wata sanarwar da ya fitar a yau Laraba, yace bikin nadin sarautar zai gudana ne a ranar Asabar 6 ga watan Mayu.

Idan baku manta ba, Allah ya yiwa sarautar Ingila rasuwa a shekarar 2022 da ta gabata,minda aka ayyana data Charles a matsayin sabon sarkin Ingila.

Rahotanni sun ruwaito Mista Adesina yace shugaba Buhari zai halarci taron domin tataunawa makomar hadakar kasashe na Commnwealth da rawar da matasa ke takawa a fannoni daban daban.

Ban Yi Dana-sanin Ayyana Binani a Matsayin Wacce Ta Lashe Zabe Ba - Hudu

A wani labarin, kwamishinan zabe na Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa-Ari, ya ce bai yi nadamar ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna na ranar 15 ga watan Afrilun ba a jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yari Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Arewa Ta Cancanci Shugabancin Majalisar Dattawa

Yunusa-Ari ya jawo cece-kuce bayan ya bayyana Aisha Binani Dahiru ta jamìyyar APC a matsayin wacce ta lashe zabe yayin da ba a kammala tattara sakamako ba.

A tun farko, gwamnati ta bayyana neman Ari bisa zarginsa da tada hankalin al'umma a lokacin da ya ya sanar sakamakon zaben da bai kammala a jihar ta Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel