Mazauna Katsina Da Jiga-Jigan PDP Sun Yi Taron Addu’a Ga Marigayi Yar’Adua

Mazauna Katsina Da Jiga-Jigan PDP Sun Yi Taron Addu’a Ga Marigayi Yar’Adua

  • Mazauna jihar Katsina sun yi taron addu'a na musamman ga marigayi Umaru Musa Yar'adua
  • A yau Juma'a, 6 ga watan Mayu ne marigayi Yar'adua ya cika shekaru 13 da rasuwa
  • Kungiyoyin PDP ne suka shirya taron addu'an a hedkwatar jam'iyyar da ke jihar

Katsina - Mazauna jihar Katsina sun hadu da jiga-jigan jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar don yi wa marigayi Umaru Musa Yar'Adua addu'a.

Taron na daga cikin tsare-tsare domin tunawa da marigayi shugaban kasar Najeriyan yayin da ya cika shekaru 13 da mutuwa, rahoton Channels TV.

Yayin taron addu'an na musamman wanda kungiyoyin goyon bayan PDP suka shirta a hedkwatar PDP da ke Katsina, inda suka bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen shugaba kuma mai son zaman lafiya.

Taron addu'a
Mazauna Katsina Da Jiga-Jigan PDP Sun Yi Taron Addu’a Ga Marigayi Yar’Adua Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Musamman, mukaddashin shugaban kwamitin riko na PDP a jihar, Dr Abdurrahman Usman, wanda ya samu wakilcin Hon. Lawal Rufa’i Safana, ya bayyana marigayi shugaban kasa Yar'adua a matsayin abun koyi a siyasa da shugabanci.

Kara karanta wannan

Shekara 13: Yadda Katsinawa da Jiga-Jigan PDP Suka Roki Allah Ya Gafarta Wa Umaru Musa Yar'Adua

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewar:

"Ba abu mai sauki bane hada manufofinsa da halayensa. Muna addu'ar Allah ya sa wata rana mu samu wanda zai yi koyi da shi sannan a kuma jinjina masa.

"Mun yarda cewa yan Najeriya za su ci gaba da tunawa da marigayi shugaban kasa Yar'adua a kowani mataki na shugabanci da ci gaban kasar."

Da yake jawabi yayin taron addu'an, wanda ya shirya taron, Malam Hamza Jibia, ya fadawa Channels TV cewa taron, wanda irinsa ne na biyar da aka yi, an shirya shi ne don tunawa da marigayi shugaban kasar.

Gwamnan Kwara ya nadawa sahararren dan kasuwar Kaduna sarauta

A wani labari na daban, gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da nadin Alhaji Buhari Adeniyi a matsayin sabon Onijagbo na Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, PDP Ta Gudanar da Zabe, Ta Sanar da Sabon Shugaban Jam'iyya da Sakatare a Jiha 1

Sabon basaraken wanda ya kasance dan kasuwa mazaunin Kaduna, ya yi nasara ne bayan ya gwabza da sauran yan takara.

Shine zai maye gurbin tsohon Onijagbo na Ijagbo, Oba Salaudeen Fagbemi Adeyeye, wanda ya mutu a watan Disamba.

Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarauta da ci gaban al'umma, Hon. Lafia Aliyu Kora-Sabi, ne ya sanar da nadin Adeniyi a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 5 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel