Najeriya Ta Fi Kowace Ƙasa Arhar Wutar Lantarki a Duniya, Cewar FG

Najeriya Ta Fi Kowace Ƙasa Arhar Wutar Lantarki a Duniya, Cewar FG

  • Ministan wuta Abubakar Aliyu ya ce Najeriya ta fi kowace ƙasa a duniya arhar kuɗin wutar lantarki
  • Ministan ya koka kan yadda ma'aikatu ke ƙin biyan kuɗin wutar lantarkin da su ke sha akan kari
  • Kwamitin wuta ya shawarci ma'aikatar kuɗi ta riƙa cire kuɗin wutar daga asusun ma'aikatun da su ka ƙi biya

Abuja - Ministan wuta na ƙasa, Abubakar Aliyu a jiya laraba ya bayyana cewa kuɗin da ake amsa na wutar lantarki a Najeriya ya fi na ko ina arha a duniya.

Ya kuma ce duk da wannan garaɓasar da wutar ta ke da ita da kuma irin ƙoƙarin da gwamnati ta ke yi na ganin wutar ta wadaci 'yan Najeriya, mutane da dama ciki harda wasu manyan ma'aikatun gwamnati ba sa son biyan kuɗin wutar.

Kara karanta wannan

"Ba Ka Bi Na Bashin Komai": Wasu Muhimman Abubuwa 5 Da Tinubu Ya Fada Yayin Da Wike Ya Gayyace Shi

Ministan Makamashi
Ministan Makamashi Abubakar Aliyu ya ce Najeriya ta fi kowacce kasa arahar lantarki. Hoto: The Herald
Asali: Facebook

Ministan ya dai yi wannan jawabi ne jiya a Abuja a yayin wata tattaunawa da kwamitin wuta na majalisar dattawa, tare da kuma shuwagabannin wasu ɓangarori na hukumomin wutar lantarkin kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Najeriya ta fi Nijar, Benin, Mali da Senegal arhar wuta

Ya kuma ƙara da cewa a duk duniya babu waɗanda su ka kai 'yan Najeriya shan wuta da arha, musamman in aka yi la'akari da irin kuɗaɗen da ake kashewa akan gas don samar da wutar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewar a Najeriya ana siyar da ma'aunin kilowat na wutar ne akan $0.15 na dalar Amurka, wanda ya yi daidai da N105. A jamhuriyar Nijar kuwa $0.42 ne na dala, $0.23 a Benin, $0.25 a Mali, $0.28 a Senegal, sai kuma $0.27 a Burkina Faso.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Matashin Saurayi Ya Burma Wa Mahaifiyarsa Wuƙa Har Ta Mutu a Kano

Da ya ke jawabi, manajan daraktan TRCN, wato hukumar rarraba wuta ta ƙasa, Sulaiman Abdulaziz yace rashin biyan kuɗin wutar da manyan ma'aikatun gwamnati su kan yi ne ya janyo aka ɗage wutar da ake bawa kamfanonin KAEDCO na Kaduna da KEDCO na Kano daga ma'aikatar wuta ta ƙasa a kwanakin baya.

Ya ƙara da cewar duk da dai yanzu an mayar da su na wucin gadi, dole ne ya zamto an biya kuɗin wutar ga hukumar rarraba wutar ta ƙasa a cikin kwanaki 60 da aka ba su dama.

Kamata ya yi a riƙa cirewa daga Asusun ma'aikatun da su ka ƙi biya

Sai dai a na shi ɓangaren, shugaban kwamitin majalisar na ɓangaren wuta Sanata Gabriel Suswam, da kuma wasu daga cikin mambobin kwamitin irin su Sanata Adamu Aliero da Yusuf sun bada shawarar cewa kamata ya yi ma'aikatar kuɗi ta ƙasa ta riƙa cirewa daga asusun ma'aikatun da suka ƙi biyan kuɗin, kamar yadda Punch ta samu.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Obi? Tsohon Shugaban Kasa Ya Roki Alfarma 1 Wurin Yan Najeriya Kan Shari'ar Zaben 2023

Zamu yi tofin Allah tsine ga masu son a kafa gwamnatin wucin gadi

A wani labarin kuma, wasu fastoci a jihar Ribas sun sha alwashin yin tofin Allah tsine ga duk masu ƙoƙarin ganin an kafa gwamnatin riƙon ƙwarya maimakon rantsar da sabuwar gwamnati.

Malaman cocin sun ce duk masu irin waɗannan kiraye-kirayen na ƙoƙarin lalata dimokuraɗiyya ne wanda hakan idan su ka cigaba na iya janyo mu su fushin Ubangiji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel