Yanzu Yanzu: Yari Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Arewa Ta Cancanci Samar Da Shugaban Majalisar Dattawa

Yanzu Yanzu: Yari Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Arewa Ta Cancanci Samar Da Shugaban Majalisar Dattawa

  • Zababben sanata Abdul’Aziz Yari, ya saka labule da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Yari ya bayyana cewa yankin arewacin Najeriya ya cancanci a mika masa shugabancin majalisar dattawa
  • Ya ce bai kamata a yi la'akari da addini na kabilanci wajen raba mukamai a majalisar dokokin tarayya ta 10 ba

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma zababben sanata, Abdul’Aziz Yari, ya bukaci jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ta duba kokari wajen rabon mukamai a majalisa ta 10 ba tare da la'akari da kabilanci ko addini ba.

Yari ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Lahadi, 30 ga watan Afrilu, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jirgin Shugaban Kasa Ya Lula Kasar Waje Domin Samun Gyara Na Musamman

Abdul'Aziz Yari da Shugaba Buhari
Yanzu Yanzu: Yari Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Arewa Ta Cancanci Samar Da Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: Punch
Asali: UGC
"Ina shawartan jam'iyyar cewa su duba kokari wajen rabon mukamai ba wai addini ba. Saboda addini baya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma baya cikin manufofi da kundin tsarin mulkinmu."

Arewa ta cancanci samar da shugaban majalisar dattawa, Yari

Yari, wanda ya kasance daya daga cikin zababbun sanatocin da ke neman shugabancin majalisar dattawa, ya bayyana cewa arewa ce ta fi bayar da kuri'u don tabbatar da nasarar APC a zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Saboda haka, ya ce ya kamata a ba yankin daman samar da shugaban majalisar dattawa na gaba.

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

"Kowa ya san rawar ganin da muka taka, duk da kasancewar sauran mutane na tunanin muna da namu. Amma mun zabi jam'iyya wacce ta ba APC damar sake kwace kujerar shugabanci.
"Don haka, muna cewa ya kamata jam'iyya ta yi abun da ya dace. Kuma wadanda suke cewa 'Musulmi da Kirista' ya kamata su yi taka tsan-tsan sosai. Iliminmu a siyasa ya wuce wannan a yanzu."

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ja Hankalin Atiku da Obi, Ya Faɗi Abinda Ya Rage Musu Kan Zaben 2023

Kungiyoyin goyon bayan Tinubu a arewa sun tsayar da Betara don zama kakakin majalisar wakilai

A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyoyin goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu, zababben shugaban kasa a jihohin arewa 19 sun ayyana goyon bayansu ga Hon Aliyu Muktar Betara, a matsayin wanda suke so ya zama kakakin majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel