Tashin Hankali Yayin Da Dalibar 400L a Uniben Ta Mutu Tana Cikin Barci

Tashin Hankali Yayin Da Dalibar 400L a Uniben Ta Mutu Tana Cikin Barci

  • Wata ɗalibar ajin ƙarshe a jami'ar Benin da ke a jihar Edo, ta kwanta dama tana tsaka da barcin ta
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa ɗalibar lafiyar ta sumul ƙalau lokacin da ta kwanta barci, amma saidai aka wayi gari aka yi arba da gawarta
  • Lamarin mutuwar ɗalibar ba ƙaramin gigita sauran abokanan kwanan ta yayi ba, waɗanda suka yi ƙoƙarin ceto ta

Jihar Edo - Wani abin baƙin ciki ya auku a ranar Lahadi, yayin da wata ɗalibar ajin ƙarshe a jami'ar Benin, Maria Precious Tunde, ta mutu a cikin barcin ta.

A cewar rahoton Tribune, majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya auku ne a ɗakin kwanan ɗalibar a ƙauyen Ekosodin, wanda ya ke a wajen makarantar.

Dalibar ajin karshe a Uniben ta mutu
Hoton Maria Precious Tunde, dalibar da ta mutu a Uniben Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

An tattaro cewa marigayiya Maria, har zuwa mutuwar ta ranar Lahadi, ɗaliba ce a ajin ƙarshe a tsangayar ilmi wacce ke a harabar Ugbowo ta jami'ar.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Gaskiya Ta Bayyana Dangane Da Batun Sanya Labulen Peter Obi Da Bola Tinubu

An kuma bayyana cewa Maria lafiyar ta ƙalau ta ke ƙafin ta kwanta barci da daddare, sai dai ba ta farka ba da safiyar ranar Lahadi, wanda hakan ba ƙaramin girgiza abokan kwanan ta ya yi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar majiyoyi, dukkanin ƙoƙarin da aka yi wajen ganin ta farfaɗo ya ci tura, yayin da sauran abokanan kwanan ta suka yi arba da gawarta, inda daga bisani suka gayyato iyayenta zuwa wajen.

Igbere tv ya rahoto cewa an sanar da ƴan banga da ƴan sanda lamarin, inda nan da nan suka garzayo zuwa gidan.

A halin da ake ciki mahaifan ɗalibar sun tafi da gawarta, yayin da aka fitar da ƴan kayayyakin ta daga cikin ɗakin kwanan ɗaliban.

Wata Dalibar Jami'a Ta Fadi Ta Rasu Tana Kammala Jarabawa

Kwanakin baya rahoto ya zo kan yadda wata ɗalibar jami'a ta yanke jiki ta faɗi, tana kammala rubuta jarabawa.

Kara karanta wannan

"Zan Kwato Nasara Ta a Kotu" Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Arewa Ya Sha Alwashi

Lamarin ya auku ne kan ɗalibar mai suna Maryam Lawan Goroma, wacce ke karatun a jami'ar jihar Yobe (YSU), da ke a yankin Arewa maso Gabar, a tarayyar Najeriya.

Mutuwar ɗalibar ta zo da ban mamaki wanda ya sanya abokanan karatun ta shiga cikin yanayi na matuƙar kaɗuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel