Daliban Najeriya Da Motarsu Ta Kama Da Wuta Sun Isa Tashar Jirgin Ruwan Sudan

Daliban Najeriya Da Motarsu Ta Kama Da Wuta Sun Isa Tashar Jirgin Ruwan Sudan

  • Ɗaliban Najeriya da motarsu ta lalace a kan hanya suka kwana a shingen RSF sun isa tashar jirgin ruwa a Sudan
  • Majiya ta ce ɗaliban guda 9 sun kwana a wurin da tayar motar Bas ɗin da suke ciki ta fashe ranar Litinin
  • Ana tsammanin akalla yan Najeriya 5,500 za'a kwaso zuwa gida daga Sudan a shirin jigilarsu da FG ta fara ranar Laraba

Ɗaliban Najeriya guda 9 da suka ƙarisa kwana a shingen binciken RSF bayan tayar motar da ta ɗauko su ta fashe ta kama da wuta, sun isa tashar jirgin ruwan Sudan.

Rahoton Channels tv ya bayyana cewa hakan ya fito ne daga wata majiya a sahsin sa ido kan kwashe jama'a daga ƙasar Sudan, wanda ya nemi a sakaya bayanansa.

Motocin kwaso yan Najeriya.
Daliban Najeriya Da Motarsu Ta Kama Da Wuta Sun Isa Tashar Jirgin Ruwan Sudan Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar jami'in, ragowar ɗaliban sun bi wata Motar Bas ɗin ta daban da Kamfanin Motocin ya turo musu, wacce ta zo da wurin zaman mutum 9 babu kowa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Motar Bas Ɗauke da Ɗaliban Najeriya 50 Daga Sudan Ta Kama da Wuta

Wane hali ɗaliban ke ciki zuwa yanzu?

A kan hanyarsu, sun gano cewa an tsare sauran yan uwansu dalibai a wani wuri, gaba kaɗan da birnin Atbara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa cikas ɗin da sauran ɗalibai waɗan da suka taho suka barsu bai shafe su ba kuma sun wuce kai tsaye zuwa tashar jiragen ruwa ta Sudan ba tare da wani ya ce musu ta tafasa sauke ba.

Sun taras da wasu 40 a tashar jirgin ruwa

Haka nan yayin da suka isa tashar jirgin ruwan, sun riski wasu ɗaliban Najeriya kusan 40, wasu daga ciki sun taho tare da iyalansu.

Rahoto ya nuna cewa waɗannan ɗalibai 40 ba su jira motocin gwamnati ba, da kansu suka tsara tafiyarsu kuma suka ɗauki nauyin kansu daga wuraren zamansu zuwa tashar jirgin.

Kara karanta wannan

Rikicin Sudan: An Hana Daruwan Dalibai 'Yan Najeriya Tsallakawa Zuwa Kasar Egypt, Dalilai Sun Bayyana

Majiyar ta ƙara da cewa ɗaliban 40 ba daga Khartoum suka fito ba, sun taho ne daga Madani, wani birni da ke kudancin Khartoum kusa da jihar Jazeera.

Zuwa yanzun an kwashe mafi yawan ɗaliban Najeriya zuwa tashar jiragen ruwan Sudan. Akalla ɗalibai 5,500 ake sa ran zasu dawo gida Najeriya daga Sudan.

Motar Bas Da Ta Dauko Daliban Najeriya Daga Sudan Ta Kama da Wuta

Idan baku manta ba mun kawo muku yadda Motar Bas Ɗauke da Ɗaliban Najeriya Da Suka Makale a Sudan Ta Kama da Wuta

Lamarin ya faru a farkon awannin wayewar garin Litinin 1 ga watan Mayu amma babu ko mutun ɗaya da ya ji rauni.

Sai dai 40 daga cikin mutum 50 da motar ya ɗebo sun samu wuri a cikin sauran motoci yayin da ragowar 10 suka kwana har gari ya waye a nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel