"Ta Iya Sarrafa Ni", Magidanci Ya Yi Wa Mai Koyon Aiki Wajen Matarsa Ciki

"Ta Iya Sarrafa Ni", Magidanci Ya Yi Wa Mai Koyon Aiki Wajen Matarsa Ciki

  • Wata mata ƴar Najeriya ta shiga damuwa bayan ta gano cewa mijinta ya yi wa mai koyon aiki a wajen ta ciki
  • Matar auren wacce ta ke da wajen gyaran gashi, ko da yaushe tana tura mai koyon aiki a wajen ta zuwa gida domin ta yi mata aikace-aikace
  • Abin takaici, sai ta fara kwantawa da mijin matar auren inda daga bisani ta samu juna biyu

Wata matar aure mai gyaran gashi ta ga ta kanta bayan ta gano cewa mai koyon aiki a wajen ta tana ɗauke da juna biyu wanda mijinta ne ya ɗirka mata.

Matar auren tana tura mai koyon aikin a wajen ta zuwa gidan ta domin ta yi mata wanki da sauran ƴan aikace-aikacen cikin gida.

Magidanci ya yiwa mai koyon aiki wajen matarsa ciki
Magidanci ya ce mai koyon aiki wajen matarsa ta iya sarrafa shi. Hoto: @Chad Hennings, Lostin Bids
Asali: Getty Images

Sai dai, a maimakon ta yi aikin da aka tura ta musamman domin ta yi, sai mai koyon aikin ta zaɓi ta zama makwafin mai koya mata aikin a wajen mijinta inda ta riƙa biya masa buƙatun sa.

Kara karanta wannan

"Ba Wayau": Kyakkyawar Budurwa Ta Damfari Wani Matashi Da Ya Ce Yana Sonta, Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa

Ta riƙa kwanciya da mijin matar duk lokacin da aka aike ta zuwa gidan har dai daga ƙarshe ta samu juna biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lokacin da matar auren ta gano abinda ya auku, sai ta lakaɗa mata dukan tsiya amma sai mijinta ya tsawatar mata inda ya bayyana yarinyar a matsayin 'gishirin rayuwar sa'.

The_Ronkee wacce ta sanya labarin a Twitter ta rubuta cewa:

"Wannan mai gyaran gashin a kan layin mu, tana tura mai koyon aiki a wajen ta zuwa gida domin ta yi mata wankin kaya, ashe kwanciya ta ke yi da mijinta, yanzu dai ta samu juna biyu, matar ta yi mata dukan tsiya, mijin ya ji labari ya zo ya lakaɗawa matar sa dukan tsiya, inda ya ce 'wannan ai gishirin rayuwar sa ce'. Mutumin ya ce yarinyar da jinin ta a jika kuma ta san hannun ta akan gado, kowa sai ya ce toor."

Kara karanta wannan

Matashi Mai Samun N100k Ya Bukaci Budurwa Mai Samun N34m Ta Aje Aikinta Ta Aure Shi

"Na ɗauka cewa sun dai na tura masu koyon aiki zuwa gida domin su yi aikin gida. Saboda meyasa ina biyan kuɗi in koyi gyaran gashi a wajen ki, kuma kina tura ni inje inyi mi ki wanki da girki a gida."

Wata Matar Aure Ta Ci Tarar Mijinta 57k Saboda Ya Dawo Gida a Makare

A wani labarin na daban kuma, wata matar aure ta koyawa mijin ta mai dawowa gida a makare wani muhimmin darasi.

Matar auren ta ci mijin nata tara inda tace hakan ya zama darasi a gare shi kada ya sake makara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel