Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Titin Kaduna-Kano Kafin Ya Bar Ofis

Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Titin Kaduna-Kano Kafin Ya Bar Ofis

  • Daga dukkan alamu nesa ta zo kusa dangane da aikin titin hanyar Kaduna zuwa Kano da aka daɗe ana yi
  • Ministan Buhari, Babatunde Fashola ya tabbatar da cewa a cikin wata mai kamawa shugaba Buhari zai ƙaddamar da hanyar
  • Sai dai ministan ya ce aikin titin hanyar Kaduna zuwa Abuja ba zai kammalu ba kafin shugaba Buhari ya bar ofis

Zaria, Kaduna - Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola (SAN), ya bayar da tabbacin cewa za a kammala aikin titin hanyar Kano-Kaduna sannan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da ita kafin ya bar ofis a ranar 29 ga Mayun 2023.

Sai dai, ministan ya ce aikin sashin farko na hanyar wanda ya fara daga Abuja zuwa Kaduna zai ci gaba ko da bayan wa'adin mulkin shugaba Buhari ne, domin ba za a samu tsaiko akan kuɗin aikin ba.

Kara karanta wannan

Kano: Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Bisa Tilasta Wani Almajiri Cin Bahaya Ana Azumi

Buhari zai kaddamar da titin Kaduna-Kano wata mai zuwa
Hoton yadda ake gudanar da aikin wani sashi na titin Abuja-Kaduna-Kano Hoto: Dailynigerian.com
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust tace ministan ya bayyana hakan ne a birnin Zazzau, jihar Kaduna a ranar litinin lokacin da ya jagoranci wakilan gwamnatin tarayya domin duba yanayin yadda aikin sashi na II da na III na hanyar yake gudana.

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun yi alƙawarin kammala wannan aikin kafin ƙarshen wannan gwamnatin, kuma da yardar Allah za mu yi hakan."
"Sashi na II (Kaduna-Zaria), wanda yake da tsawon kilomita 73, za a kammala shi a ƙarshen makon nan kamar yadda ɗan kwangilar ya tabbatar mana, yayin da sashi na IIl (Zaria-Kano) za a kammala shi a wata mai zuwa."

Da aka tambaye shi ko yaya makomar sashin Kaduna-Abuja za ta kasance bayan mulkin Buhari, sai yace Nigerian Sovereign Investment Authority (NSIA) ne take biyan kuɗin aikin sashin Kaduna-Abuja saboda haka aikin zai cigaba ko waye akan kujerar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bene Mai Hawa 7 Ya Rushe, Ya Danne Danne Mutane da Yawa Ana Cikin Azumi

The Nation tace Fashola ya yi nuni da matsalar tsaron da ake fama da ita a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka kawo naƙasu wajen kammala aikin titin hanyar Kaduna-Abuja.

Gwamnatin Tarayya Za Tayi Wa Ma’aikata Karin Albashi

A wani labarin na daban kuma, gwamnatin tarayya za tayi wa ma'aikatan ta ƙarin albashi mai tsoka domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Gwamnatin tarayyar za ta ƙara wa ma'aikatan kaso 40% na albashin su, amma sai shugaba Buhari ya amince.

Asali: Legit.ng

Online view pixel