INEC Ta Ce Abdulsamad Dasuki Ne Ya Lashe Zabe a Mazabar Tambuuwal/Kebbe a Majalisar Wakilai

INEC Ta Ce Abdulsamad Dasuki Ne Ya Lashe Zabe a Mazabar Tambuuwal/Kebbe a Majalisar Wakilai

  • Rahoto daga jihar Sokoto ya ce, dan takarar majalisar wakilai ta kasa a PDO ne ya kashe zaben da aka gudanar
  • A baya, sanata Aliyu Wamakko ya sake samun nasarar komawa kujerarsa ta sanata a Sokoto ta Arewa
  • A jihar Yobe, dan takarar APC, Ibrahim Bomai ya samu nasarar zama sanata a zaben da aka kammala

Jihar Sokoto - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta alanta dan takarar PDP, Abdulssamad Dasuki a matsayin wanda ya lashe kujerar dan majalisa a mazabar Kebbe/Tambuwal a Sokoto.

Wannan na fitowa ne daga bakin baturen zabe, Farfesa Abubakar Sidiq Muhammad, kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.

A cewarsa, dan takarar na PDP ta yi nasara ne da kuri’u 47,317, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na APC, Kokani Bala Kebbi mai kuri’u 34,282.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: Jerin 'yan takarar da suka yi nasara a zaben jiya Asabar

Idan baku manta ba, Dasuki ya kasance dan majalisar wakilai na tarayya a mazabar tsakanin 2015 zuwa 2019 kafin Kokani ya kwace kujerar a 2019.

Sokoto: Abdulsamad ya lashe zabe
Jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin da ake ciki, tsohon kwamishinan kudin jihar zai sake komawa majalisa a karo na biyu don maye gurbin Kokani Bala Kebbe.

Tsohon gwamna Wamakko ya lashe zabe

A bangare guda, Aliyu Magatakarda Wamakko ya sake lashe kujerar sanata a karo na uku a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.

Wannan na zuwa ne a sakamakon zaben cike gurbi da aka gudanar a jiya Asabar 15 ga watan Afrilu, kamar yadda rahoto ya bayyana.

An ruwaito cewa, Wamakko ya lallasa dan takarar jam'iyyar PDP kuma mataimakin gwamnan jihar a wannan zaben na bana.

A tun farko, an dakata da tattara sakamakon zaben majalisar dokokin tarayya a Sokoto saboda matsalolin tsaro da aka samu.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Bayan dogon kai ruwa rana, Ado Doguwa ya lallasa dan tsagin Kwankwaso

Ibrahim Bomai ya zama sanata a Yobe

A wani labarin kuma, kun ji yadda dan takarar APC na sanata a mazabar Yobe ta Kudu ya lashe zaben bana.

An sanar da Ibrahim Bomai ne ya lashe yawan kuri'un da aka kada a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Faburairu da kuma 15 ga watan Afrilu.

Jam'iyyar APC na ci gaba da samun kujerun siyasa a Najeriya, duk da kuka da ake da ita game da mulkinta na wadannan shekarun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel