Yanzu Yanzu: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kebbi

Yanzu Yanzu: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kebbi

  • Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta yi nasarar lashe zaben gwamna a jihar Kebbi
  • INEC ta ayyana Nasiru Idris ya matsayin zababben gwamnan jihar Kebbi a ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilu
  • Idris ya doke babban abokin adawarsa na PDP, Aminu Bande da tazarar kuri'u 48,285

Kebbi - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress ( APC), Dr Nasiru Idris, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi.

Baturen zaben gwamnan a jihar, Farfesa Sa’idu Yusuf, ya ce dan takarar na APC ya lashe zaben da kuri'u 409,225, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Idris ya lallasa babban abokin hamayyarsa, Aminu Bande na jam'iyyar Peoples Democratic party (PDP) wanda ya samu kuri'u 360940 a zaben.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: Jerin 'yan takarar da suka yi nasara a zaben jiya Asabar

Zababben gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris
Yanzu Yanzu: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kebbi Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Channels TV ta rahoto cewa tazabar kuri'u 48,285 tsakanin zababben gwamnan da babban abokin hamayyarsa na PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda baturen zaben gwamnan Kebbi ya ayyana APC a matsayin wacce ta lashe zabe

Yayin da yake ayyana dan takarar na APC a matsayin wanda ya yi nasara, baturen zaben ya ce:

"Ni, Saidu Yusuf baturen zaben gwamnan jihar Kebbi na ayyana Nasiru Idris na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan bayan ya samu jimilar kuri'u 409225 kuma ya cike dukkan ka'idojin da doka ya tanadar."

Ku tuna cewa an fara gudanar da zaben gwamnan a ranar 18 ga watan Maris, amma INEC ta ayyana shi a matsayin wanda bai kammalu ba saboda barkewar rikici da zartawar kuri'u.

Ya ce jimilar mutum 95,897 aka yi wa rijista a zaben cikon yayin da aka tantance masu zabe 40,186.

Kara karanta wannan

Dawo-dawo: PDP ta sake samu kujerar majalisa wakilai ta tarayya a jihar Sokoto

"Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 20,967 a zaben yayin da PDP ta samu kuri'u 17,960.
"Jimilar kuri'un da APC ta samu shine 409225 yayin da PDP ta samu 360940. Jimilar kuri'u masu inganci ya kasance 781478, wadanda aka yi watsi da su 19082 yayin da jimilar kuri'un da aka kada ya kama 800560,” in ji baturen zaben.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai jami'in hulda da jama'a na hukumar INEC na kasa kuma kwamishinan wayar da kan masu zabe, Mista Festus Okoye, ya ce sakamakonm cikon zaben na Kebbi ya nuna cewa INEC za ta iya yin abun da yake shine daidai.

Tambuwal ya lashe zaben sanata mai wakiltan Sokoto ta kudu

A wani labarin, mun ji cewa hukumar INEC ta ayyana Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto a matsayin zababben sanata mai wakiltan yankin Sokoto ta kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel