Jam'iyyar APC ta kara lashe kujerar Sanata a Arewacin Najeriya

Jam'iyyar APC ta kara lashe kujerar Sanata a Arewacin Najeriya

  • Jam'iyyar APC ta kara lashe kujerar Sanata yayin da INEC ta fara bayyana sakamakon zabukan da ta kammala yau Asabar
  • Baturen zabe ya ayyana ɗan takarar APC, Diket Plang, a matsayin wanda ya ci zaɓen Sanatan Filato ta tsakiya
  • Mista Plang, zai haɗe da sauran zababbun Sanatoci 2 daga jihar Filato, waɗanda suka lashe zabe tun farko a inuwar PDP

Plateau - Hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Honorabul Diket Pland na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan shiyyar Filato ta tsakiya.

Da yake bayyana sakamakon zaben a Pankshin, hedkwatar shiyyar jihar Filato ta tsakiya, baturen zaɓe na INEC, Dakta Jima Lar, ya ce ɗan takarar APC ne ya samu kuri'u mafi rinjaye.

Diket Pland.
Jam'iyyar APC ta kara lashe kujerar Sanata a Arewacin Najeriya Hoto: Diket Pland
Asali: Twitter

Dakta Lar ya bayyana cewa Honorabul Plang ya samu jimullan kuri'u 131,129, wanda suka ba shi damar lashe zaɓen, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Jam'iyyar APC ta sake cin kujerar sanata a wata mazabar Yobe

Ya ce babban abokin karawar Plang, watau Mista Yohanna Gotom, na jam'iyyar PDP, ne ya zo na biyu da kuri'u 127,022, yayin da Garba Pwul na Labour Party ya tashi da kuri'u 36,510.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalaman baturen zaben ya ce:

"Kasancewar Honorabul Diket Plang ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben kuma ya cika duk wasu sharuɗɗa da ka'aidojin da doka ta tanada, na ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Filato ta tsakiya."

Plang, tsohon mamban majalisar dokokin jihar Filato, wanda ya wakilci mazaɓar Pankshin, a yanzu zai zarce majalisar dattawan Najeriya a matsayin Sanatan Filato ta tsakiya.

Zai haɗe da sauran takwarorinsa, Simon Mwadkwon, wanda ya lashe zaben Sanatan Filato ta Arewa da Napoleon Bali, wanda ya ci Sanatan Filato ta kudu dukkansu a inuwar PDP.

Vanguard ta rahoto cewa tun da fari INEC ta ayyana APC a matsayin jam'iyyar da ta lashe zaɓen Sanatan jihar Yobe ta kudu.

Kara karanta wannan

Gaskiya 4 Da Suka Bayyana Game da Gwamna da Aishatu Binani a Zaɓen Jihar Adamawa

Yan daba sun mamayi wurin zaɓe a Kano

A wani labarin kuma Yan Daba Sun Kai Hari Rumfar da Ake Zabe Yau a Jihar Kano

Wasu yan daba sun tarwatsa masu kafa kuri'a a wata rumfar zabe da ke yankin karamar hukumar Fagge a jihar Kano amma jami'an tsaro sun fatattake su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel