Ayyuka 14 da Buhari Ya Yi wa Kudu da Babu Shugaban da Ya Kama Kafarsa a Tarihi

Ayyuka 14 da Buhari Ya Yi wa Kudu da Babu Shugaban da Ya Kama Kafarsa a Tarihi

  • Duk da suka da musamman ‘yan adawa su ke yi wa shugaba Muhammadu Buhari, gwamnatinsa tayi zarra a wasu wurare a shekaru 8
  • Masu nazari su na cewa daga cikin inda gwamnatin Muhammadu Buhari tayi fice akwai gina abubuwan more rayuwa domin al’umma
  • Tolu Ogunlesi yana cikin masu ba shugaban Najeriya shawara, ya na kokari wajen wanke gwamnatin mai gidansa daga masu suka

Abuja - Da yake fayyace zare da abawa kamar yadda ya saba a shafin Twitter, Tolu Ogunlesi ya jero wasu daga cikin alheran gwamnatin nan.

Mista Ogunlesi ya fado irin ayyukan da Buhari ya yi wa jihohin Kudu, ganin har gobe ana sukarsa a yankin da cewa bai tsinana masu komai ba.

Daga lokacin da Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa zuwa yau, an samu:

1. Katuwar sabuwar tashar ruwa da aka gina a Legas.

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Aika Wasika, Yana Nemawa Sanatan da Aka Samu da Laifi a Ingila Alfarma

2. Sababbin tashoshin kan tudu da aka soma kuma aka karasa

3. Mallaka tashar ruwan Onitsha kuma ya fara aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga haka akwai:

4. Sabon sansanin sojojin ruwa a Imo.

5. Sabon sansanin sojojin sama a Enugu.

6. Sasanta rikicin kamfanonin raba wuta na Enugu da sauran ayyukan TCN.

7. Kammala gidan tarihin tunawa da Zik bayan shekaru 20.

Buhari
Tashar ruwa a Legas Hoto: www.nigeriainfo.fm
Asali: UGC

Hadimin yake cewa kafin zuwan Buhari, babu wata tashar kan tudu da ake da ita a duk Najeriya.

Yanzu maganar da ake yi, akwai manyan tashoshin kan tudu bakwai wanda ake iya sauke kaya a kasar nan, dukkansu su na karkashin ‘yan kasuwa ne.

A cewar Mai ba shugaban na Najeriya shawara, tun 1999 zuwa yau, babu wani shugaban da ya yi wa Kudu maso gabashin Najeriya kokarin irin uban gidansa.

Daga ciki akwai:

1. Naira biliyan 2 ta karkashin tsarin Sukuk domin gina hanyoyin yankin.

Kara karanta wannan

Sanusi, El-Rufai, Gbaja da Jerin Sauran Mutanen da Ake Tunanin Tinubu Zai Tafi da Su

2. Aikin hanyar Enugu zuwa Onitsha.

3. Doka da aka kawo da ta ware $10m domin ‘yan kasuwa su gina matatu.

4. Hanyar tashin jirgin kasa da aka yi a Enugu

5. Dala miliyan 5 da aka ware domin binciken lafiya a Umuahia.

6. Biyan fansho ga 'yan sandan Biyafar bayan shekaru 20.

7. Gadar Neja

Zargin sata a hukumar NIMASA

Tsawon shekaru ana shari’a tsakanin Gwamnatin tarayya da Patrick Akpobolokemi a kotu, an ji labari lauyoyin EFCC sun samu yadda su ke so a zaman karshe.

Ana tuhumar Dr. Patrick Akpobolokemi da satar N725m da samun filin a Banana Island lokacin da ya samu mukami, kotu ta ce gwamnati ta fara rike dukiyoyin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng