NFIU: Gwamnoni Za Su Yi Fadan Karshe da Gwamnatin Buhari a Kan Dokar Cire Kudi

NFIU: Gwamnoni Za Su Yi Fadan Karshe da Gwamnatin Buhari a Kan Dokar Cire Kudi

  • Gwamnonin jihohi za su yi taro a kan takunkumin da Hukumar NFIU ta kakaba masu a Najeriya
  • NFIU ta hana Gwamnoni cire tsabar kudin tsaro daga asusun banki domin yakar rashin gaskiya
  • Matakin da aka dauka bai yi wa Jihohi dadi ba, za su yi zama da ICPC, EFCC, CBN da FRIS a yau

Abuja - Gwamnonin jihohi za su samu sabani da hukumar NFIU a game da yadda za a rika cire kudin harkar tsaro daga cikin baitul-malin gwamnati.

Wani rahoto na The Nation ya nuna cewa gwamnoni 36 za su yi zama da hukumomin yaki da rashin gaskiya kan yadda za a kula da kudin.

Haka zalika za ayi zama ta kafar yanar gizo da hukumar FIRS da kuma babban bankin Najeriya duk a kan batun domin a iya shawo kan sabanin.

Kara karanta wannan

Kamar bandaki: Gidan da budurwar da ta gaji da biyan haya ta gina ya girgiza intanet

Hukumar NFIU ta kasa ta ce gwamnoni za su iya kashe dukiyar tsaro duk yadda suka ga dama amma da sharadin cewa ba tsabar kudi za a batar ba.

Sharadin da NFIU ta sa

Ba mu ce Gwamnonin jihohi ba za su iya yin amfani da kudinsu ba. Abin da aka ce shi ne su yi abin da ya kamata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dole ne sai sun kashe kudin tsaro a tsabar su? Idan biyan kudi su ke so su yi, za su iya aikawa, ba dole sai tsaba ba.

- Hukumar NFIU

Gwamnoni
Taron Gwamnonin Jihohi Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

An kira taro a yau

Jaridar ta ce jim kadam bayan NFIU ta maka takunkumin wajen cire zunzurutun kudi daga asusun gwamnati, kungiyar NGF ta shirya yin taro.

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta fitar da sanarwa ta bakin Kakakinta, Malam Abdulrazaque Bello-Barkindo cewa za ayi muhimmin zama yau.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnoni 36 Za Su Gana Da EFCC, CBN Don Yanke Shawara Kan Kudin Tsaro

Darekta Janar ta NGF, Asishana Okauru ta ce za ayi zaman ta yanar gizo ne domin kowa ya halarta, hakan yana nufin ba sai an halarra a Abuja ba.

Bello-Barkindo yake cewa daga cikin wadanda aka halarta zuwa wajen taron akwai wakilan hukumomin EFCC, ICPC, FIRS da kuma bankin CBN.

A wannan zama da za ayi, ana sa ran cin ma matsaya a kan yadda gwamnati za ya rika karbar haraji.

An fusata Abdullahi Ganduje

Rahoto ya zo cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce shawarwarin da zababben Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yake badawa ba su da gindin zama.

Baya ga haka Gwamnan Kano mai barin gado ya ce za kalubalanci gajerar nasarar da NNPP ta samu a kotun zabe, tuni dai Abba Gida Gida ya yi masa raddi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng