Sojojin Najeriya Hudu Sun Kwanta Dama a Wani Mummunan Hatsari a Bauchi

Sojojin Najeriya Hudu Sun Kwanta Dama a Wani Mummunan Hatsari a Bauchi

  • Hukumar FRSC ta tabbatar da rasuwar sojoji huɗu a wani hatsari da ya rutsa da motar da suke ciki a jihar Bauchi
  • Kwamandan FRSC, Yusuf Abdulahi, ya ce sun samu rahoton abinda ya faru a kauyen Lago, karamar hukumar Darazo
  • Ya ce haɗarin ya faru sanadiyyar fashewar tayar mota, yanzu haka Fasinja 13 na kwance a Asibiti

Bauchi - Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar sojojin Najeriya guda huɗu a wani hatsarin Mota da ya auku a kauyen Lago, jihar Bauchi.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa mummunan haɗarin ya auku ne a Lago, kan babban Titin Bauchi zuwa Maiduguri, a cikin jihar Bauchi ranar Alhamis.

Hadarin mota.
Sojojin Najeriya Hudu Sun Kwanta Dama a Wani Mummunan Hatsari a Bauchi Hoto: leadership
Asali: UGC

Kwamandan FRSC na shiyyar jihar Bauchi, Yusuf Abdulahi, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga 'yan jarida a Bauchi ranar Alhamis, 30 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Kitmurmura: An rincabe a APC a jihar Arewa bayan dan takarar ya sha kasa a zaben gwamna

Ya ce sauran mutane 13 da ke cikin motar sun ji raunuka kala daban-daban a hadarin wanda ya rutsa da mota ɗaya da Sojojin ke tuƙawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar kwamandan, Sojojin na kan hanyarsu ta zuwa babban birnin tarayya Abuja a Motar haya Toyota Bus mai lamba ASU 363-XA, "Domin gudanar da wani aiki," lokacin da haɗarin ya rutsa da su.

Kwamandan ya ce:

"Mun samu labarin wani haɗari da ya auku da tsakar rana wajen ƙarfe 1:36 na rana a nisan kilomita 21 a kauyen Lago, Titin Darazo-Kari, yankin ƙaramar hukumar Darazo."
"Nan take jami'anmu suka hanzarta zuwa wurin domin aikin ceto cikin mintuna 20. Sun ɗauke waɗanda lamarin ya shafa zuwa babban Asibitin Darazo domin ba su magani da tabbatarwa."
"A Asibitin ne kwararren likita ya tabbatar da mutuwar mutum huɗu, sauran mutane 13 kuma sun ji raunuka daban-daban, wasu sun bugu a kai wasu kuma sun samu karaya."

Kara karanta wannan

Mota Ɗauke da Fursunoni Ta Haddasa Babban Tashin Hankali a Babban Birnin Jiha

"Bayanan da muka tattara sun nuna cewa Sojoji ne da ke kan hanyar zuwa wani aiki a birnin tarayya Abuja, a halin yanzun an maida wasu Asibiti na musamman a Bauchi."

- Yusuf Abdulahi

Shugaban FRSC a Bauchi ya ƙara da cewa haɗarin ya auku ne sakamakon fashewar tayar mota, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Jiragen sama biyu na sojoji sun rikito ƙasa

A wani labarin kuma Jiragen Helikwafta 2 Na Rundunar Soji Sun Yi Hadari, Ana Fargabar Rasa Rayuka da Yawa

Mahukunta a kasar Amurka sun tabbatar da afkuwar haɗarin wasu jirage biyu yayin da su ke shawagin ɗaukar horo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel