Motar Gidan Yari Ta Haddasa Hatsari, Matasa Sun Fusata a Jihar Osun

Motar Gidan Yari Ta Haddasa Hatsari, Matasa Sun Fusata a Jihar Osun

  • Wata motar gidan gyaran hali ɗauke da Fursunoni ta haddasa kace nace da zanga-zanga a Osogbo, babban birnin Osun
  • Ganau ya ce lamarin ya faru ne lokacin da Direban motar ya ƙi bin umarnin Fitilar ba da hannu, ya kutsa kai ya bigi motar haya
  • Lamarin ya jikkata mutum biyu kuma nan take mutane suka ɓarke da zanga-zanga har sai da 'yan sanda suka zo suka tarwatsa su

Osun - An shiga yanayin tashin hankali da ɗar-ɗar a Osogbo, babban birnin jihar Osun ranar Alhamis yayin da wata motar gidan Yari ta haddasa hatsari a kan Titi.

Punch ta tattaro cewa motar wacce ke ɗauke da Fursunoni zuwa babbar Kotun jiha, ta bugi wata ƙaramar motar haya, lamarin da ya yi sanadin raunata mutum biyu.

Motar gidan gyaran hali.
Motar Gidan Yari Ta Haddasa Hatsari, Matasa Sun Fusata a Jihar Osun Hoto: punchng
Asali: UGC

Wani ganau da abun ya faru a kan idonsa ya ce Direban motar gidan gyaran halin ne ya ƙi bin Fitilar da ke baiwa matafiya hannu a kan Titin, wacce ta nuna lamar ya tsaya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Sojojin Najeriya 4 Sun Mutu a Hanyarsu Ta Zuwa Abuja, Wasu 13 Sun Jikkata

Ya ce sanadin haka ne Direban motar da ta ɗauko Fursunonin ya bugi ƙaramar Motar Bas ta haya, Direba da fasinja ɗaya da ke ciki suka jikkata sakamakon haka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nan take lamarin ya haddasa zanga-zanga, inda direbobin motocin haya da wasu fusatattun matasa suka toshe babbar mahaɗar titunan Olaiya Junction da sunan zanga-zanga.

Zuwa yanzun da muke haɗa maku wannan rahoton, jami'an rundunar 'yan sandan da suka kai ɗauki wurin da lamarin ya faru sun tarwatsa masu zanga-zanga.

Rahotanni sun bayyana cewa da zuwan dakarun 'yan sanda wurin, suka fara harba barkonon tsohuwa, bisa tilas mutanen da suka taru a hanyar suka yi takansu.

Ripples Nigeria ta tattaro cewa a halin yanzun jami'an yan sanda da dakarun DSS busa jagorancin DPO na caji Ofis ɗin Dugbe, CSP Akinloye Oyegade, suna wurin don kare abin ka iya faruwa.

Kara karanta wannan

Akwai Yunwa: Gwamnatin Tarayya Da Bayyana Adadin Yaran Dake Galabaita a Najeriya Saboda Rashin Abinci Mai Kyau

Haɗarin mota ya lakume rayukan Sojoji 4

A wani labarin kuma Sojojin Najeriya Hudu Sun Kwanta Dama a Wani Mummunan Hatsari a Bauchi

Sojoji 4 sun rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a yankin karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi. Kwamandan FRSC yace lamarin ya auku a ƙauyen Lago, titin Bauchi-Maiduguri. A halin yanzun an kai sauran mutane 13 da suka ji raunuka Asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel