Daga Ranar da Aka Rantsar Dani Zan Fara Aiki, Inji Zababben Gwamnan Jihar Katsina Radda

Daga Ranar da Aka Rantsar Dani Zan Fara Aiki, Inji Zababben Gwamnan Jihar Katsina Radda

  • Zababben gwamnan jihar Katsina ya bayyana kadan daga abubuwan da ya sanya a gaba na alheri ga al’ummar jiharsa
  • Ya ce zai fara aiki ne tun daga ranar da aka rantsar dashi a matsayin gwamnan jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma
  • Bola Tinubu na ci gaba da shan kira kan ya yaki yunwa da fatara a mulkinsa, musamman duba da yanayin da ake ciki yanzu

FCT, Abuja - Zababben gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Raddda ya yi alkawarin fara aiki tukuru daga ranar farko da ya karbi mulkin jihar.

Radda ya ba da wnanan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Lahadi 26 ga watan Maris.

Ya kuma bayyana manufofinsa na tafiyar da mulki wadanda ya sanyawa suna ‘Bulding a Future’, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Dikko Radda ya bayyana manufarsa idan ya karbi mulki
Dikko Umaru Radda kenan, zababben gwamnan jihar Katsina | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Abubuwan da Radda zai mai da hankalinsa a kai

A cewarsa, babban abin da zai fara mai da hankali a kansa shine, tabbatar da daidaita hanyoyin samar da kudin shiga na jihar da kuma tsara jihar ta fuskar filaye da gine-gine.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, tun kafin ya tsaya takarar gwamna yake da tsarinsa a kasa, don haka yanzu dauka zai yi kawai don fara aik babu kama hannun yaro.

A cewarsa:

“Manufarmu itace gyara bangaren tsaro. Muna son magance lamarin rashin tsaro a jihar Katsina. Wannan shine babban abin da muka sa a gaba.”

Zan gyara jihar Katsina da ma'aikatanta

A bangare guda, zababben gwamnan ya ce zai yi kokarin tabbatar da an yi gyara a fannin da ya shafi aikin gwamnati.

Ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta samar da hanyoyin horar da ma’aikatan gwamnati domin su samu kwarewar tafiyar da harkokin jihar yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Zababben ‘Dan Majalisa Ya Sha da Kyar, An Kusa Kashe Shi, An Kona Motarsa Kurmus

Har ila yau, a tattaunawar tasa ya yi tsokaci kan dalilin da yasa Tinubu bai kawo kuri'u mafi yawa a jihar ta Katsina ba, rahoton Daily Trust.

An roki Tinubu ya mai da hankali ga yakar yunwa da fatara

A wani labarin, kun ji yadda kungiyar Muslmai ta Al-Habibiyyah ta nemi Bola Tinubu ya gaggauta kawo mafita ga ‘yan Najeriya ta fannin tattalin arziki da walwala.

Kungiyar ta ce, ‘yan Najeriya a fusace suke, suna bukatar a yaki talauci da yunwa don samun damar gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

A baya, Tinubu ya yi alkawarin kawar da yunwa a Najeriya a lokacin da yake kamfen din zama shugaban kasa, gashi dai Allah ya ba shi nasara a zaben na bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.