Wanda Baiji Bari Ba Zaiji Woho: EFCC Cafke Masu POS 80 a Ondo

Wanda Baiji Bari Ba Zaiji Woho: EFCC Cafke Masu POS 80 a Ondo

  • Hukumar ta EFCC na cigaba da tabbatar da cewar, dokar takaita kudi da zurga-zurgan su ta tabbata ta hanyar taimakawa CBN ganin ana bin dokar.
  • EFCC takai sumame a jihar ta Ondo inda ta cafke masu sana’ar POS guda 80 tare da yin awon gaba dasu
  • Hukumar ta EFCC tace haramun ne a siya kudi da kudi sannan a siyar da kudin a amshi kudi saboda haka ta kama duk masu yin hakan

Dokar kudi da CBN ya saka na cigaba da samun goyon baya daga hukumomi irin su EFCC.

A kalla masu sana’ar POS guda 80 hukumar EFCC ta kama a Akure, Babban birnin jihar Ondo.

Hukumar ta gudanar da aikin kamen ne a Kudancin Akure wato Akure North da kuma Akure South.

EFCC Badge
Wanda baiji bari ba Zaiji Woho: EFCC Cafke Masu POS 80 a Ondo Hoto: Legit.ng

Rahotanni dai sun tabbatar da cewar, Hukumar ta EFCC ta kama wadannan masu POS ne sakamakon siyan kudi da kuma saida kudin da caji maras kan gado.

Kara karanta wannan

Toh fa: DSS ta hango matsala a Najeriya, ta ba 'yan kasa shawarin kariya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar The Nation ta ruwaito cewar, sai da EFCC ta matsawa masu sana’ar ta POS , sannan suka sanar mata yadda suke samun kudin da suke gudanar da kasuwancin nasu.

Wata majiya tace, masu POS din da kansu suka tabbatar da cewar suna sayan kudin ne daga bankuna, wanda daga baya sai su caji abokan huldar su da mugun tsada.

Kamar yadda majiyar ta tabbatar:

“Sun kama akalla masu POS 80 a yankin Oja Oba. Da zarar sunzo inda kake, zasu tambaye ka a ina kake samun kudi, kuma nawa kake amsa kafin ka bada kudi, sannan suce maka ka kaisu inda kake samo kudin.”
“Wasu masu POS din sai suka samu labari tun kafin aje wajen su, dajin haka sai suka gudu suka bar shagunan su.”
“Yanzu Yanzu wani mai POS ma yana tsaye anan yana bawa wani abokin harkallar sa kudi, wata mata tazo ta tambaye shi nawa yake amsa a duk naira 1000.”

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama 'yan POS 80 da ke gallazawa 'yan Najeriya, suna siyar da kudi

Hukumar EFCC ta Kara Gurfanar da Yaron Tsohon Shugaban PDP a Kotu a Kan Zargin ‘Satar’ Kudi N2.2bn

Hukumar EFCC a karkashin jagorancin Bawa, dake kokarin yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta kara shiga kotu tare da Nasir Ali Mamman

Shidai Nasir Ali Mamma da Christian Taylor hukumar EFCC na zargin su ne da wata badakala dake da alaka da bada tallafin mai.

Karar ta dan Kanal Ahmadu Ali, yanzu haka tana gaban kotun dake kula da aikata laifuffuka na musamman da take da zamanta a Legas, kuma ana sa ran za’a cigaba da shari’ar a watan Mayu mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel