Yan Sanda Sun Haramta Yin Zanga-Zanga a Fadin Jihar Nasarawa

Yan Sanda Sun Haramta Yin Zanga-Zanga a Fadin Jihar Nasarawa

  • Rundunar jihar Nasarawa ta bi takwararta na jihar Kaduna wajen hana zanga-zanga a fadin jihar
  • Kakakin yan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel, ya ce sun dauki matakin ne domin hana karya doka da oda
  • A cewarsa bayanan sirri da suka samu kan tsaron jihar ya nuna ba za su iya daukar kowani nau'i na zanga-zanga ba don dorewar zaman lafiya

Nasarawa - Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta haramta gudanar da kowani nau'i na zanga-zanga a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Lahadi, 26 ga watan Maris, kakakin yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa rundunar yan sandan ta yanke hukuncin ne don hana karya doka da oda da zaman lafiyar da jihar ke ciki a yanzu.

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Yan Sanda Sun Haramta Yin Zanga-Zanga a Fadin Jihar Nasarawa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewarsa, rahoton sirri kan tsaro a jihar ba zai iya daukar kowani nau'i na zanga-zanga ba a jihar, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Ku gargadi yaranku a kan fita zanga-zanga, yan sanda ga iyaye

Hakazalika, runduna yan sandan ta shawarci iyaye da su tabbatar da yaransu basu karya dokar nan ba domin duk wanda aka kama kan haka za a kwamushe shi da kuma hukunta shi daidai da doka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar na cewa:

"Rundunar yan sandan jihar Nasarawa na burin samar da jama'a cewa an haramta duk wani nau'i na zanga-zanga a fadin jihar. Don haka, an haramta duk wani zanga-zanga kowani iri.
"Rundunar yan sandan ta dauki wannan hukunci domin hana karya doka da oda da kuma ci gaba da dorewar zaman lafiyar da ake ciki a jihar a yanzu; kasancewar bayanan sirri kan tsaro ba zai iya ci gaba da daukar kowani nau'i na zanga-zanga ba a jihar.
"Saboda haka ana shawartan iyaye da su tabbatar da yaransu basu karya wannan umurni ba domin duk wanda aka kama za a damke shi sannan a hukunta shi daidai da doka.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam El-Rufai Ta Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan Siyasa Dake Shirin Ta Da Yamutsi

Jaridar Punch ta rahoto cewa tun bayan zaben gwamna a jihar wanda gwamna mai ci, Abdullahi Sule ya yi nasarar zarcewa a kan kujerarsa, magoya bayan jam'iyyar PDP mai adawa da suka hada da mata da matasa suna ta zanga-zanga.

Masu zanga-zangar sun kuma nemi hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INECO ta sake duba zaben.

Makiyan Najeriya ne ke kira ga tunbuke shugaban INEC, Ogah

A wani labari na daban, mun ji cewa wani dan majalisa mai wakiltan mazabar Ikwo/Ezza ta kudu, Kwamrad Chinedu Ogah, ya ce makiyan Najeriya ne masu neman a tsige shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel