Bidiyo: Matashi ya kai Budurwa ta Zabi Gwanjo Kala-kala Kafin Ranar Masoya ta Duniya

Bidiyo: Matashi ya kai Budurwa ta Zabi Gwanjo Kala-kala Kafin Ranar Masoya ta Duniya

  • Irin kaunar da wani mutumi 'dan Najeriya ya nuna ga budurwarsa da yadda ta yi masa martani ya narkar da zukatan 'yan yanar gizo
  • Matashin mai hangen nesa ya kai budurwarsa wata kasuwa cikin Port Harcourt don yin siyayya ranar Masoya na wannan shekarar
  • Matar ta matukar yin farin ciki, inda ta yi siyayyar gwanjo a karo na biyu a kasuwar yayin da masoyin nata ya zuba mata ido

Domin bikin Ranar Masoya ta 14 ga watan Fabrairu, wani mutumi 'dan Najeriya mai hangen nesa ya fitar da budurwarsa waje don siyan kayyakin gwanjo.

Siyan Gwanjo
Bidiyo: Matashi ya kai Budurwa ta Zabi Gwanjo Kala-kala Kafin Ranar Masoya ta Duniya. Hoto daga @litosman001
Asali: TikTok

Gwanjo wata kalmace da 'yan Najeriya ke amfani da ita matsayin suturu na sawa da aka yi amfani da su da kayayyakin sawa irinsu takalma da jakunkuna.

Wani mutumi mai amfani da kafar TikTok ne ya wallafa faifan bidiyon da tsokacin:

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matar Aure ta Fita da ATM din Mijinta, Tayi Waddaka da Kudinsa Son Ranta

"Barazana kafin zagayowar Ranar Masoya. Wanda shi ne babban barazana."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya fara bidiyon ne da gabatar da takardu biyu da aka rubuta "siyayyar gwanjo" a gefe wanda shi kadai zai iya gani yayin da umarceta da ta dauka.

A bidiyo na biyu, ya nuna wata kakykyawar budurwa tana zabar gwanjo a Port Harcourt yayin da masoyin nata ya zura ma ta ido yana ma ta bidiyo.

Daga bisani suka dauki hoto tare. Bidiyon mai daukar hankali ya janyo martani masu tsuma zuciya daga soshiyal midiya.

Martanin 'yan soshiyal midiya

user841069299581 ya ce:

"Gaskiya tana da kyau, ina kaunar fatar ta."

Preshy ta ce:

"Ko dai gwanjo mai matsayi na farko ko kuma na biyu amma dai gwanjo ne babu zabi."

giftedlasson ya ce:

"Kuma tana farin ciki, ka ga matar aure. Ubangiji ina rokonka ina zan samu irin wannan matar."

Kara karanta wannan

Kada Ku Kashe Ni, Zan Tona Asiri: Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Ta Zauce, Bidiyon Ya Girgiza Jama'a

Favy Felix ya ce:

"Idan nayi soyayya da irin ki, zamu iya amfani da kudin haya mu siya gwanjo. Zan so isar da sakon da nayi niyyar zan nuna kamar ban gani ba."

viccky261 ta ce:

"Wannan irin soyayya haka hmmm hmmm."

Sdat ya ce:

"Haka ne 'dan uwa.. ka samu mace kyakkyawa.. wadannan ba kawai gwanjo bane matsayi na farko ne.."

CutestZahra ya ce:

"Bata da wani zabi abun dariya za ta zabi gwanjo ne kawai."

'Dan Najeriya bude gidan biredi bugu kato a Amurka

A wani labari na daban, wani 'dan Najeriya ya bude katafaren gidan biredi bugun kato a Amurka.

A halin yanzu yana da rasssa sama da biyar bayan wasu da suka amsa sunan gidan biredin suka bude irinsa a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel