Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Yan Banga Sama da 50 a Zamfara

Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Yan Banga Sama da 50 a Zamfara

  • 'Yan bindigan daji sun halaka dakarun ƙungiyar 'yan banga 51 a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara
  • Kansilan yankin ya ce har yanzun gawarwakin mutanen na cikin daji an gaza ɗauko su saboda tsoron makasan
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara ya ce babu wanda ya kaiwa gwamnati rahoton abinda ya faru

Zamfara - 'Yan ta'adda sun kashe aƙalla 'yan Banga 51 a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ranar zaɓen gwamna da 'yan majalisar dokokin jiha.

Jaridar vanguard ta rahoto cewa har yanzun gawarwarkin jami'an tsaron ƙungiyar 'yan bangan da aka kashe na cikin Daji saboda mutane na tsoron 'yan ta'addan.

Harin ta'addanci a Zamfara.
Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Yan Banga Sama da 50 a Zamfara Hoto: vanguard
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru a ƙaramar hukumar Maru da ke cikin jihar Zamfara.

Kansilan yankin, Honorabul Iliya Darega, ya shaida wa manema labarai cewa 'yan bangan sun tattaru daga kauyuka uku, suka fita Sintiri ranar zaɓe 18 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rikici Ya Kara Tsananta a Kano, An Wargaza Akwatunan Zabe Sama da 10

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, Jami'an ƙungiyar 'yan bangan sun rasa rayukansu ne yayin da 'yan ta'addan suka musu kwantan bauna, suka kashe su.

Yace sun faɗa wa hukumar 'yan sanda, Sarakunan yankin da sauran hukumomin tsaro kan abinda ya faru da kuma gawar jami'an da ke cikin jeji, amma har yanzun ba su yi komai ba.

"Mun damu matuƙa, har yanzu gawarwakin suna cikin jeji, muna son yi musu jana'iza amma mutane suna fargabar makasan 'yan ta'adda da ke cikin jejin," inji shi.

Yayin da BBC Hausa ta tuntuɓi kwamishinan yaɗa labarai na Zamfara game da lamarin, ya ce ba su da masaniya kan abinda ya faru.

Jami'am 'yan sandan da ke aiki a yankin sun bayyana cewa har yanzun suna dakon cikakken bayanin abinda ya faru.

Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren 'yan ta'adda a shiyyar arewa maso yamma tsawon wasu shekaru da suka gabata.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Harin Wurin Raba Kayayyakin Zabe, Sun Tafka Barna

Yan bindiga sun kai mummunan hari Neja

A wani labarin kuma Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake da Wasu 2, Sun Sace Sama da 60 a Neja

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙuyukan kananan hukumomin Munya da Paikoro, kuma maharan sun kwashe awanni babu wanda ya tanka musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262