Karancin Takardun Naira Na Shafar Ramadan, Kungiyar Izala Ta Fada Wa Gwamnatin Buhari

Karancin Takardun Naira Na Shafar Ramadan, Kungiyar Izala Ta Fada Wa Gwamnatin Buhari

  • Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da karin takardun kudi don rage radadi a cikin watan azumi
  • Alhaji Hassan Gwani shi ne wanda ya yi rokon in da ya ce karancin takurdun kudi na jefa mutane cikin matsi musamman wajen siyen kayan masarufi
  • A gefe guda, mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci musulmi su yi wa kasa addua a wannan wata na azumi a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja

Bauchi - Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah reshen Jihar Bauchi, a ranar Juma'a, ta roki gwamnatin tarayya da ta samar da wadatattun takardun kudi lokacin watan Ramadan.

Shugaban kwamitin Tafsir, masallacin JIBWIS na kasuwar shanu, Alhaji Hassan Gwani, shi ne ya yi rokon yayin bude karatun tafsirin azumin Ramadan na bana, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Zabe: Dalilin Da Yasa Shugabannin Najeriya Da Ke Kan Mulki Ke Shan Kaye A Akwatunan Aso Rock

Buhari
JIBWIS ta fada wa Buhari cewa rashin kudi na shafar Ramadan. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

''Azumi ya sake zagayowa kuma kudaden da ake al'amuran yau da kullum ba sa samuwa wanda hakan ya jefa mutane cikin wahalar siyen abun da su ke da bukata.
''Idan gwamnatin tarayya na son a karbi wannan tsarin, ya kamata ta yawaita sabbin takardun kudi don mutane su samu na kashewa.''

A gefe gudu, kwamitin zartarwar na gwamnatin tarayya ya taya musulmi murnar zagayowar watan Ramadan.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha, shi ya aike da sakon taya murnar a madadin kwamitin zartarwar ranar Juma'a, a wata sanarwa da daraktan yada labarai, na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Mista Willie Bassey ya fitar.

Atiku Abubakar ya shawarci al'ummar musulmi su yi wa Najeriya addu'ar zaman lafiya a Ramadan

A na shi bangaren, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi kira ga musulmi da su yi amfani da lokacin azumi don neman shiriya su kuma yi addu'o'in neman zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Atiku, wanda shi ne dan takarar jam'iyyar PDP a zaben da aka kammala, ya bada shawarar a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce:

''Abu ne a bayyane irin abubuwan da ke kunshe cikin watan Ramadan su ne abin da mu ke bukata don magance matsalolinmu, a matsayin mu na daidaiku da kuma kasa''.

A gefe guda, shugaban kwamitin majalisar dattawa, kan al'amuran shari'a da yancin dan adam, Sanata Opayemi Bamidele, ranar Juma'a ya bukaci musulmi da su yi amfani da watan azumi don yakar munanan halaye.

Bamidele ya ce:

''Abu mafi muhimmanci, yan uwanmu musulmai ya kamata su dauki wannan watan ba wai iya na tsarkake kai ba. Su yi wa kasa addu'a kan sha'anin tsaro, rashawa, kabilanci, da nuna bambancin da ke addabar kasar nan ya ke kuma raba kan al'umma.''

Shugaba Buhari ya sabunta nadin Idris Musa a matsayin shugaban NOSDRA

A wani rahoton, kun ji cewa Idris Musa ya sake samun daman cigaba da jagorantar hukumar kiyayye kwararewar man fetur da kawo daukin gaggawa, NOSDRA.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hadi Sirika Ya Daukarwa Yan Najeriya Alkawari 1 Gabanin Mulkin Buhari Ya Kare

Asali: Legit.ng

Online view pixel