Zabe: Dalilin Da Yasa Shugabannin Najeriya Da Ke Kan Mulki Ke Shan Kaye A Akwatunan Aso Rock

Zabe: Dalilin Da Yasa Shugabannin Najeriya Da Ke Kan Mulki Ke Shan Kaye A Akwatunan Aso Rock

  • Tun 2015, shugaban kasa mai ci ba ya iya lashe akwatunan zaben da ke fadar shugaban kasa saboda wasu dalilai
  • Al'amrin da ke zama abin ban mamaki ga kowanne bangare, wanda ke zama abin murna ga yan adawa duk ba hakan ne ke nuna sakamakon karshe na zabe ba
  • Majiyoyi sun bayyana cewa rashin kokarin gwamnati da kuma rashin gamsuwa da salon mulkin gwamnati ne ya janyo ma'aikatan fadar ke kokarin canja gwamnati

Daga 2015 zuwa yanzu, shugaban kasa mai ci ya na shan kaye a akwatunan zaben da ke fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa, Abuja, a hannun jam'iyyun adawa.

Duk da dai sakamakon zaben akwatunan ba shi ya ke bayyana wanda ya yi nasara ba, lamarin na matukar bayar da mamaki ga magoya bayan yan takarar shugabancin kasa, wanda ba ma a birnin tarayya, Abuja su ke kada kuri'a ba.

Kara karanta wannan

Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya

Magoya bayan wanda su ka lashe akwatunan, a mafi yawan lokuta, su na murna da sakamakon a matsayin kyakkyawar alama kafin a sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasa.

Aso Rock Villa
Harabar fadar shugaban kasar Najeriya. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka lamarin ya kasance ko a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023 na shugaban kasa. Sakamakon akwatuna 10 da aka tattara ya nuna Peter Obi, dan takarar jam'iyyar LP, a matsayin wanda ya lashe akwatunan fadar shugaban kasa.

Obi ya samu kuri'a 809 in da ya kayar da Asiwaju Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa mai ci Muhammadu Buhari, wanda ya kada kuri'arsa tare da mataimakansa da iyalansa a Daura, da ke Jihar Katsina.

Tinubu ya yi na biyu da kuri'a 318, yayin da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'a 258 wanda hakan ya ba shi damar zuwa na uku a akwatunan da ke fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

A duk akwatun, da su ka hada da 121, titin Kofo Abayomi, kusa da Officers' Mesa da 131, da ke kallon Pilot Gate, a gidan gwamnati, Obi ya kayar da abokan takararsa.

Haka lamarin ya ke a shekarar 2019 dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, ya samu kuri'un da su ka haura na shugaban kasa Buhari, wanda shi ne dan takarar jam'iyyar APC a zaben, a cikin fadar shugaban kasa.

Yayin dan takarar jam'iyyar PDP ya samu kuri'a 525, Buhari ya samu kuri'a 465 a akwatu mai lamba 022.

Sai dai, Buhari ya samu kuri'a fiye da abokin hamayyarsa a akwatu mai lamba 021, ya samu kuri'a 548 fiye da abokin karawarsa mai kuri'a 505.

Jimilla, dan takarar jam'iyyar PDP ya samu kuri'a 1,030 fiye da ta shugaban kasa 1,013, da bambancin kuri'a 17.

A 2015, dan takarar jam'iyyar PDP, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ke mulki a lokacin, ya fadi daya daga cikin akwatunan fadar shugaban kasar a hannun abokin hamayyarsa na APC, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Karancin Takardun Naira Na Shafar Ramadan, Kungiyar Izala Ta Fada Wa Gwamnatin Buhari

A akwatu mai lamba 022, Buhari ya samu kuri'a 348 yayin da Jonathan ya samu kuri'a 302.

Jonathan ya samu kuri'a 293 yayin da Buhari ya samu kuri'a 265 a akwatu ta biyu da ke fadar shugaban kasa, mai lamba 021.

A sakamakon karshe da aka tattara daga akwatunan biyu, Jonathan ya sha kayi a hannun Buhari, wanda ke takara karo na hudu a lokacin, inda ya samu jimillar kuri'a 595 yayin da Buhari ke da kuri'a 613. Sanar da sakamakon ya janyo murna ga magoya bayan jam'iyyar APC.

Jonathan ya lashe zaben a duk akwatunan biyu a zaben 2011. Ya kayar da Buhari, wanda shi ne dan takarar jam'iyyar CPC da ta narke a wancan lokacin, da fiye da rabin kuri'un da aka kada.

A daya daga cikin akwatunan, wanda nisanta bai wuce mita 100 daga Pilot Gate ba, Jonathan ya samu kuri'a 630 yayin da Buhari ke da kuri'a 318.

Kara karanta wannan

"INEC Ta Yi Kuskuren Ayyana Abba Gida-Gida Matsayin Zababben Gwamnan Kano", Masu Sa Ido Kan Zabe

Me yasa shugaban kasa ke faduwa a fadar shugaban kasa

Daily Trust a ranar Lahadi ta ruwaito cewa ana ganin da yawa daga cikin masu kada kuri'a a fadar shugaban kasa a matsayin mataimaka na musamman, ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Daya daga cikin ma'aikatan fadar da ya nemi a sakaya sunan shi ya ce da yawa da yawan masu rijista a yankin ma'aikatan fadar ne yayin da wasu ke rijista a matsayin mazauna yankin.

An ruwaito cewa sakamakon zaben shugaban kasa a fadar baya rasa nasaba da rashin tabuka abin arziki da gwamnati ke yi a yankin.

Wani ma'aikacin fadar ya ce:

''Sun ki zabar APC a 2023 saboda mutane na shan wahala. Mafi rinjayen masu kada kuri'a a fadar shugaban kasa ma'ikata ne da ke gwamnatin APC ba ta yi kokari ba, musamman da ake tsaka da wahalar mai da karancin kudi.''

Wani ma'aikacin ya tuna cewa Jonathan ya fadi a fadar a 2015 saboda mutane ba su ji dadin halin da Najeriya ta tsinci kanta a wannan lokacin.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba, Inji Fayose

A cewar majiyar.

''Mutane sun gamsu cewa bai kamata ya cigaba da shugabanci ba."

Daily Trust a ranar Lahadi ta ruwaito daga wata majiyar cewa sakamakon zaben na nuni da yadda al'ummar yankin ba su gamsu da shugabancin gwamnati mai mulki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel