A Yau INEC Za Ta Ci Gaba da Tattara Sakamakon Zabe a Jihohin Abia da Enugu

A Yau INEC Za Ta Ci Gaba da Tattara Sakamakon Zabe a Jihohin Abia da Enugu

  • Hukumar zabe ta ce za a ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a jihohi Abia da Enugu a yankin Kudancin Najeriya
  • An dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna a wasu kananan hukumomin jihohin ne saboda samun matsala da aka yi
  • Rikicin siyasa a jihar Taraba ya kai ga mutuwar wasu jami’an ‘yan sanda da ke bakin aiki a lokacin da ake tattara sakamakon zabe

Najeriya - Hukumar zabe zaman kanta (INEC) ta ce za a ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a kananan hukumomi uku na jihohin Enugu da Abia a yau Laraba 22 ga watan Maris.

Hukumar zaben ta dage ci gaba da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Obingwa ta Abia da kuma Nsukka da Nkanu East a jihar Enugu, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: INEC Ta Kammala Nazari Kan Sakamakon Zaben Gwamnoni 28, Ta Ɗauki Mataki Kan Jihohi 2

Festus Okoye, kwamishinan yada labarai na INEC ne ya sanar da batun ci gaba da tattara sakamakon zaben a ranar Laraba da rana a cikin wata sanarwa.

Za a ci gaba da tattara sakamakon zaben Abia da Enugu
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Bayanai daga hukumar zabe ta INEC

A cewar sanarwar:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Hukumar ta gama nazarinta. Don haka, za a ci gaba da tattara sakamakon zaben jihohin Abia da Enugu a yau 22 ga watan Maris 2023.
“Hukumar ta yaba da hakuri da fahimtar da mutane suka yi a jihohin biyu har muka gama da tattara dukkan abubuwan da ake bukata.”

Yadda ala dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna

A baya an dage ci gaba da tattara sakamakon zaben ne biyo bayan suka da ake yiwa INEC daga bangaren ‘yan takarar gwamna a jam’iyyu daban-daban, rahoton The Nation.

Jam’iyyar PDP a jihar Enugu ta zargi hukumar zabe da saba ka’ida, inda tace hukumar ba ta da hurumin dakatar da tattara sakamakon zaben da aka riga aka kammala.

Kara karanta wannan

An Shiga Zullumi Bayan INEC Ta Ki Amincewa Da Sakamakon Zaben Jihohi 2, Ta Bayyana Dalili

Zaben 2023 na gwamnoni a Najeriya ya zo da tsaiko da cece-kuce, lamarin da yasa a wasu jihohin aka yi tashin-tashina da rikici bayan siyasa.

An hallaka ‘yan sanda a wurin tattara sakamakon zabe

A wani labarin, kun ji yadda aka hallaka wasu jami’an ‘yan sanda da ke bakin aiki a ofishin hukumar zabe da ke jihar Taraba.

An ruwaito cewa, wasu sojoji ne suka hallaka jami’an tare da jikkata wasu biyu bayan barkwar rikici a tsakaninsu.

Ya zuwa yanzu, an sanar da sakamakon zaben wasu jihohi, wasu kuma ana ci gaba da kai ruwa rana kan sahihancin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel