Yadda Wata Mata Ta Auri Maza 3, Take Rayuwa Dasu a Cikin Gida Daya

Yadda Wata Mata Ta Auri Maza 3, Take Rayuwa Dasu a Cikin Gida Daya

  • Nellie ta auri kanin mijinta bayan da mijin nata da suka haifi yara biyu ya rasu a wani mummunan hadarin mota
  • Daga baya, matar ta sake auren wasu mazan biyu a lokuta mabambanta, inda suke rayuwa a wuri guda suna cin duniyarsu
  • Nellie ta ce, tana iya gamsar dasu mazan nata uku gaba dayansu kuma tana da yakinin ba za su yi mata kwange ba

Ba sabon abu bane, a addinance ma ya halasta namiji ya auri mace fiye da daya, amma ga mace, hakan babban lamari ne.

Wata mata da ke siyar da motoci ta yi shuhura a yankinsu bayan da ta auri maza uku, kuma take tare dasu a gida daya.

Mazajen nata, Jimmy, Danny da Hassan basu da zabin da ya wuce su zama abokai saboda suna da mata guda daya da suke rayuwa da ita.

Yadda ta auri maza 3, take gamsar dasu
Hotunan Nellie da mazajenta 3 | Hoto: Afrimax English
Asali: Youtube

Ta fadi tarihinta

Ta shaidawa Afrimax English cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Sunana Nellie, ni ce a kauyen nan ta yi suna tare da maza na uku. Na rayuwa da wadannan mutanen a matsayin maza na tsawon shekara uku. Ina da mijin da muke tare tsawon shekaru takwas amma ya rasu a hadarin mota.
"Bayan rasuwarsa, an barni da kaninsa, Hassan, sai muka ci gaba da rayuwa a gida daya wanda muka rayu da mijina da ya rasu. Ya nuna min kauna, kuma na kamu da kaunarsa.”

Daya daga cikin mazan ya magantu

Danny, wanda bai jima da kammala karatunsa ba kuma bai ma da sana’ar yi a lokacin da ya gamu da Nellie, ta nuna masa soyayyarta, ta kuma kai shi gidanta inda sauran mazan suka karbe shi.

A bangaren Jimmy, gamuwa dashi ta yi yana cikin bacin rai da mummunan yanayin soyayya, sai ta nemi sanin matsalolinsa.

Ya ce:

“Ina bukatar wacce za ta lallaba ni ta kuma fada min kalamai masu dadi, sannan ina bukatar wacce zan ke yi mata magana.
“Ta bani tarihin rayuwarta. A wancan ranan muka rabu, amma muka ci gaba da kasancewa abokai. Mun amince da rayuwarmu a yadda muke muka ci gaba da rayuwa a matsayin miji da mata.”

Ina gamsar da su duka, cewar Nellie

Nellie ta yi alfahari da cewa, tana iya tabbatar da sanya mazajen nata farin ciki, kuma tana da yakinin ba za su yi mata kwashe-kwashen ‘yan mata ba.

Hakazalika, ta ce tana yi musu adalci yadda ya kamata, domin komai iri daya take yi musu daidai gwargwado.

A cewarta, kowa na da dakinsa cikin mazajen nata, don haka ta san yadda suke raba kwana da ranakun rayuwarsu.

A baya ma an samu matar da ta auri maza biyu, kuma take rayuwa tare dasu a inuwa daya, lamari mai ban mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel