“Diya Tagari”: Uba Ya Fashe Da Kuka a Wajen Auren Diyarsa Yayin da Ta Durkusa Ya Sa Mata albarka

“Diya Tagari”: Uba Ya Fashe Da Kuka a Wajen Auren Diyarsa Yayin da Ta Durkusa Ya Sa Mata albarka

  • Bidiyon wani uba yana kuka wiwi da hawaye a wajen baikon auren diyarsa ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • Yayin da diyar mutumin ta tashi tsaye don barin wajen, mahaifin nata ya bar hawayensa sun kwaranya a kan kuncinsa
  • Jama'a da dama da suka yi martani ga bidiyon sun ce da gani diyar tasa yarinya ce tagari tun da har mahaifinta ya zubar da hawaye

Wani uba ya gaza rike hawayen idanunsa a yayin baikon auren diyarsa a cikin wani bidiyo da shafin @ariyike_alaga ya wallafa.

Hawaye na ta kwarara daga idanun mutumin zuwa kuncinsa yayin da diyar tasa ta durkusa a gabansa.

Mahaifiyar yarinyar ma ta karaya amma sai ta boye fuskarta a cikin tafukan hanayyenta. Mahaifin yarinyar ya gaza dago idanunsa yayin da yake yi wa diyar tasa bankwana.

Kara karanta wannan

“Zan Fasa Auren”: Kyakkyawa Amarya Ta Ajiye Kunya Ta Tika Rawa Iya Son Ranta a Wajen Bikinta, Bidiyon Ya Yadu

Uba na kuka a wajen bikin diyarsa
“Diya Tagari”: Uma Ya Fashe Da Kuka a Wajen Auren Diyarsa Yayin da Ta Durkusa a Gaban Shi Hoto: @ariyike_alaga
Asali: TikTok

Yanayi mai tsuma zuciya a wajen shagalin biki

An nuno lokacin da mutumin ke sanyawa diyar tasa albarka. Bidiyon ya tsuma zukata da dama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutane da dama da suka garzaya sashin sharhi a bidiyon sun ce lallai da gani yarinyar diya tagari ce ga iyayenta, kuma suna bakin cikin rabuwa da ita.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya tattara martani fiye da 500 da 'likes' fiye da 44,000.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

eaglemoneyjktya ce:

"Diya tagari ce iyayenta ke kuka a lokacin aurenta."

KVÑG JÖHÑ ta ce:

"Mahaifina na da taurin rai idan ya yi wa ni ko kanwata kuka na tafi a tsaye mutumin da bai taba yi wa kansa kuka ba."

Omo_shalewa ta ce:

"Idan mahaifina ya yi kuka haka a ranar aurena watakila sai dai mutum ya koma gidansu fa zan bi mahaifina zuwa gida ne."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Kyakkyawar Amarya Ta Yi Amfani Da Bakinta Wajen Daura Girki Ranar Aurenta Ya Dauka Hankali

Eddie Wd ya ce:

"Abun da ke faruwa kenan idan kika zamanto diyar kirki."

Ada Anambra ta ce:

"Mahaifina ya yi ta maza sosai kuma yana farin cikin zan yi aure amma abubuwa sun chanja a lokacin da zan tafi gida tare da mijina..ya ki yarda sannan ya ce ba zan tafi ba."

Ango ya hau tsani don yin daidai da tsawon matarsa a wajen bikinsu

A wani labari, mun ji cewa wata yar dirama ta faru a wajen daurin wani aure lokacin da ango ya haye kan wani dan karamin tsani domin ya sumbaci matarsa wacce ta fi shi tsawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel