Na Ƙagu In Tafi, In Ji Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Na Ƙagu In Tafi, In Ji Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

  • Buhari ya bayyana cewa ya matsu ya bar kujerar shugaban kasa a yayin da ya ke karbar bakuncin jakadiyar Amurka mai barin gado a fadarsa
  • Buhari ya ce ya gamsu da yadda aka gudanar da zabe duk da akwai yan takarar da bai ji dadin faduwarsu ba amma ya ce mutane sun fara gane karfinsu
  • Shugaban ya kuma yabawa jakadiyar Amurka mai barin gado, inda ya bayyana sun cimma muhimman abubuwa tsakanin Amurka da Najeriya tsahon zamanin jakadancin na ta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada bukatarsa ta barin mulki, Daily Trust ta rahoto.

A lokuta da dama a baya, Buhari ya sha fadin cewa 29 ga watan Mayu kawai ya ke jira ya mika mulki.

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari yana tafiya. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba, Inji Fayose

Da ya ke jawabi a taron bankwana da jakadiyar Amurka mai barin gado, Mary Beth Leonard, a fadar shugaban kasa a Abuja ranar Talata, shugaban Najeriya ya ce, ''na kagu in tafi''.

Ya fadi haka lokacin da ya ke amsa tambaya daga Leonard.

Ya kara da cewa ya shirya zama ''babban manomi'' da zai dinga aiki a gonakinsa ya na kula da dabbobinsa sama da 300 a Daura, mahaifarsa a Jihar Katsina.

Buhari, wanda ya bayyana gamsuwa da yadda yan Najeriya su ka nuna muhimmancin dimukradiyya ta hanyar zabar wanda ran su ya ke so a zabukan da aka kammala, ya ce lallai an samu cigaba ta wannan fannin a Najeriya.

''Mutane sun fara gane karfin su. Bayar da damar zaben adalci da gaskiya, ba wanda zai gaya mu su abin da za su yi. Ban ji dadin rashin nasarar wasu daga cikin yan takarar ba. Amma naji dadi da yadda mutane su ka yi zabinsu, su ka zabi wanda ya ci da kayar da wanda ya fadi.''

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

''Da chanjin kudi, babu kudin da za a siyi kuri'a amma duk da haka, na fadawa ma su kada kuri'a da su karbi kudin su kuma zabi abin da ran su ya ke so,'' in ji shugaban kasar.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa ya gamsu da matakin da ya dauka a lokacin zabe na yin shiru ba tare da tsoma baki ta kowacce hanya ba.

Buhari, ya kuma yabawa jakadiyar Amurka mai barin gado, bisa irin abubuwan da aka cimma tsakanin Amurka da Najeriya tsawon zamanta shekara uku da rabi.

Shugaba Buhari ya sabunta nadin Idris Musa a matsayin shugaban NOSDRA

Idris Musa ya sake samun daman cigaba da jagorantar hukumar kiyayye kwararewar man fetur da kawo daukin gaggawa, NOSDRA.

Ma'aikatar ta Muhalli ta sanar da hakan a ranar Litinin a shafinta na dandalin Twita (@FMEnvng).

Asali: Legit.ng

Online view pixel