Gwamna Umahi Ya Nada Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka

Gwamna Umahi Ya Nada Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka

  • Saura watanni 2 da yan kwanaki wa'adin mulkinsa ya kare, gwamna Umahi ya naɗa sabbin hadimai 30
  • Gwamnan jihar Ebonyi ya naɗa mutanen ne domin su rika bibiyar ayyukan da gwamnati take gudanarwa a faɗin jihar
  • Ya bukaci hadiman su zage dantse su yi amfani da wannan lokacin wajen kara gogewa a sha'anin mulki

Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Davud Umahi, ya naɗa sabbin hadimai 30 domin su ƙara karfafa shugabanci mai kyau ga mazauna jihar yayin da ya rage watanni 2 ya sauka.

Jaridar PM News ta rahoto cewa yayin rantsar da mutanen a Abakaliki ranar Laraba, gwanna Umahi ya umarci sabbin hadiman su maida hankali wajen aiki tun a matakin farko.

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi.
Gwamna Umahi Ya Nada Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Hoto: Dave Umahi
Asali: UGC

Ya roki mutanen da ya naɗa da su yi aiki a kananan hukumomin jihar domin tabbatar da romon Demokaradiyya ya isa ga talakawa ba tare da nuna wariya ba.

Kara karanta wannan

Bayan Sake Komawa Kan Kujerar Sa, Gwamnan PDP Yayi Jawabi Mai Daukar Hankali Kan Masu Adawa Da Shi

Ya yi bayanin cewa ya zakulo su kuma ya naɗasu waɗannan mukaman ne bayan la'akari da gudummuwar da suka bayar lokacin suna matsayin Ko'idinetoci a kananan hukumomi daban-daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Wasu daga cikin manyan ayyukan da muke su ku sa wa ido sun haɗa da, Jirgin sama, faɗaɗa Titin Ring-Road, Fenti da kwalliya, da kuma filin wasan kwallo da aikin gina gadojin sama."
"A koda yaushe ku riƙa aiki da kwanishinan ayyuka, Sufuri da gidaje wajen sauke nauyin da muka ɗora muku."

Gwanna Umahi ya buƙaci hadiman su yi amfani da ragowar watanni biyu da suka rage su ƙara samun gogewar aiki domin ci gaban jihar Ebonyi.

Jerin sunayen sabbin hadimai 30

Legit.ng Hausa ta tattaro muku sunayen mutane 30 da gwamna Umahi na APC ya naɗa a matsayin hadimai, ga su kamar haka;

Kara karanta wannan

Sun Ki Allah Ya Nufa: Yadda Na Kusa Da Ni Suka Ci Amanata a Lokacin Zabe, Gwamnan APC Yayi Bayani Mai Sosa Rai

1. Augustina Nwaovu

2. Obinna Nwaiboko

3. Baron Anya

4. Innocent Eluu

5. Chima Okoro Eze

6. Victor Nwaobasi

7. Elias Igwe

8. Ikechukwu Nwafor

9. Kingsley Akam

10. Theodore Iheta

11. Emmanuel Ekuma

12. Martin Oga

13. John Ogodo

14. Afulike Uchechukwu

15. Justice Agu

16. Misis Blessing Nweze

17. Victor Nwoke

18. Chijioke Nwuzor

19. Uche Nwankpuma

20. Misis Roseline Nkwuda

21. Patrick Enyi

22. Tochukwu Uzor

23. Misis Sharon Umahi

24. Ejike Agbo

25. Stephen Ogenyi

26. Arthur Ude Umanta

27. Ikechukwu Anoke

28. Uchenna Ugwuta

29. Sebastian Ojiogu

30. Ama Okoro.

PDP ta lashe zaben gwamna a Enugu

A wani labarin kuma INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamna a Jihar Enugu Mai Cike da Ruɗani

Bayan kai ruwa rana, baturen zaɓe ya ayyana ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a matsayin wanda ya samu nasarar zama zaɓaɓɓen gwamna a jihar Enugu.

Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan INEC ta bayyana wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Abiya.

Kara karanta wannan

2023: Zababben Gwamna a Arewa Ya Aike da Saƙo Mai Ratsa Zuciya Ga Mutanen da Ba Su Zabe Shi Ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel