Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Bauchi da Gombe a Arewacin Najeriya

Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Bauchi da Gombe a Arewacin Najeriya

A yau tafe ranar zaben gwamnoni a Najeriya, ba a bar jihohin Gombe da Bauchi a baya a yankin Arewa masu Gabashin kasar.

A jihar Bauchi, dan takarar jam'iyyar APC, AM Sadeeq Abubakar ne zai gwabza da gwamna mai, Bala Muhammad na jam'iyyar PDP da dai sauran 'yan takarar jam'iyyun siyasa.

A jihar Gombe kuwa, Muhammadu Inuwa Yahaya, gwamnan APC mai ci ne ke kokarin kare kujerarsa daga mamayan 'yan takarar jam'iyyar PDP, Muhammad Jibril Danbarde da kuma na NNPP Muhammad Khamisu Mailantarki.

Legit.ng Hausa na nan kai tsaye a lunguna da sako a Najeriya don tattaro muku yadda taje kayawa a zaben na bana, ku biyo mu a nan don jin yadda ake ciki a jihohin Gombe da Bauchi.

Jama'a na ta fitowa a Gombe don kada kuri'u, suna tattaki

Rahotanni daga jihar Gombe sun nuna cewa, an samu jama'ar gari da yawa da suka fito domin kada kuri'unsu a zaben da ke gudana a yau Asabar.

Mazauna unguwannin Madaki, Sabon Layi a Bolarim Herwagana da Kumbiya-kumbiya sun fito domin zabe.

Hakazalika, an ga mutane da yawa na tattakin zuwa rumfunan zabe a wasu unguwannin jihar ta Gombe, rahoton Premium Times.

An ga jami'an tsaro sun isa wasu rumfunar zaben tun misalin karfe 6:55 na safe don tabbatar da tsaro a jijar.

Haka nan, masu kada kiri'u da yawa ne suka fito kada kuri'un a unguwanni daban-daban na jihar.

Zabe a karamar hukumar Kaltungo ta jihar Gombe

An fara kada kuri'u a rumfa ta 022 a karanar hukumar Kaltunga ta jihar Gombe da ke Arewa maso gabas.

Sai dai, an ga turawan zaben na zaune a kasa suna aikinsu babu kujera ko teburin zama a yi aikin.

Ana ci gaba da zabe cikin tsanaki a jihar Bauchi

Ya zuwa karfe 9:03 na safe, tuni an fara zabe a Kofar Yalawa da ke gundumar Sakwa a karamar hukumar Zaki ta jihar Bauchi.

Jami'an zabe sun iso Kataugum, za a fara zabe

Jami'ai da turawan zabe sun iso gundumar Nasarawa B, rumda ta 041 da ke Katagum a jihar Bauchi.

An fara kada kuri'u a Darazau, jihar Bauchi

Da misalin karfe 8:48 aka fara kada kuri'u a gundumar Wahu rumfa ta 001 da ke karamar hukumar Darazau a jihar Bauchi.

Jami'an tsaro da turawa zabe sun iso rumfunar zabe a Makama Sarkin Barki ta Demsa a Bauchi

Da misalin karfe 7:29 ne ma'aikatan zabe da jami'an tsaro suka iso rumfar zabe ta 002 ta Makama Sarkin Barki dake karamar hukumar Demsa ta jihar Bauchi.

Online view pixel