Kotun Koli Ya Tabbatar da Jimkuta a Matsayin Dan Takarar Sanatan APC a Taraba

Kotun Koli Ya Tabbatar da Jimkuta a Matsayin Dan Takarar Sanatan APC a Taraba

  • Kotun koli ya tabbatar da Jimkuta a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC da aka yi a jihar Taraba na sanatoci
  • An kai ruwa rana har sau uku a kotu, inda aka ba dan takarar na sanata gaskiya duba da hujjojin da ya gabatar
  • Za a yi zaben gwamnoni da ‘yan majalisu a Najeriya, amma za a hada da na wasu sanatoci da ‘yan majalisun tarayya

FCT, Abuja - Kotun kolin Najeriya ya tabbatar da David Jamkuta a matsayin sahihin dan takarar sanatan mazabar Taraba South a jam’iyyar APC.

A ranar Juma’a, kotun ya yi watsi da daukaka karar da dan takarar sanata Danjuma Shiddi ya yi game da sahihancin David, Channels Tv ta ruwaito.

Jimkuta ne ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar APC da aka yi a Taraba South, amma jam’iyyar ta maye gurbinsa da Shiddi, wanda ya rike kujerar majalisar wakilai.

An fadi wanda ya lashe zaben fidda gwani a Taraba
Jihar Taraba a Arewa maso Gabas | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Bai amince da maye gurbinsa ba, ya tunkari kotun tarayya a Abuja, inda ya nemi a bi kadunsa tare da mayar masa hakkinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya kasance

A tun farko, ya yi ikrarin cewa, ya ci zaben fidda gwanin jam’iyyar da kuri’u 170, inda Shiddi ya samu kuri’u 80 kacal.

Ya roki kotun da ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin tare da hana hukumar zabe ta INEC daukar Shiddi a matsayin wanda ya yi nasara.

Sai dai, bai yi nasara a kotun tarayya ba, inda daga baya tafi kotun daukaka kara, wacce ta ba shi gaskiya a matsayin wanda ya lashe zaben, Daily Post ta ruwaito.

A bangaren Shiddi, ya daukaka kara zuwa kotun koli, inda aka tabbatar da hukuncin na kotun daukaka kara na Jimkuta gaskiya a shari’ar.

A yanzu dai, kotun kolin ya tabbatar da Jimkuta a matsayin wanda ya lashe zaben, kana ta amince da zabansa a zaben da ya wakana.

Za a hada zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya a jihohi 15

A wani labarin, kun ji yadda hukumar zabe ta INEC ta bayyana za a sake zaben sanatoci a wasu jihohin Najeriya.

Hakazalika, an ce za a yi zaben ‘yan majalisun tarayya a hade da na gwamnoni saboda wasu matsalolin da suka taso.

Ba wannan ne karon farko da ake samun dage zabe a Najeriya, hakan ya sha faruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel